Tsautsayi ko son banza?

Tsautsayi ko son banza?




Muna cikin motar haya dani da wannan abokin nawa sai wani da muke zaune a seat guda ya fiddo iPhone 14 pro max, ya ce ma abokina mamansa ce ba ta da lafiya Kuma suna buqace da kudi shi ya sa ya ke son ko Dubu 75 ne don su biya kudin da za a Yi ma ta tiyata.

Ko da Aboki na ya ji an ce dubu 70 sai ya kar6i wayar ya na duba ta don ya tabbatar ko jabu ce. Amma abun mamaki sai mu ka ga komi na ta lafiya Lau ne, ga Kuma hoton gayen a wallpaper. Ko da na ga haka sai na ce ma abokina "anya wannan wayar ba ta sata ba ce?". Sai ya ce min ai ko ta sata ce in ya saye ta zai je a yi Mata flashing ne, sannan ya sake mata kes sai ya yi saurin sayar da ita.

Shapshap suka yi ciniki abokina ya nemi ragi aka sayar Masa da ita dubu hamsin. Take abokina ya Yi ma gayen tiransifa, Ni dai Ina riqe da waya a tsorace ina Tunanin ba abin da zai sa mutum ya sayar da iPhone dubu 50 in har ta sa ce.

Muka sauka daga bus din muna daga ma abokin cinikin mu hannu har suka tafi.

Muka zauna qarqashin wata bishiya abokina na qara dudduba wayar, Yana cikin dubawa sai wayar ta dauke, sai muka yi tunanin qila chaji ne, na qar6i wayar na dan duba kwatsam Kuma wayar sai ta kunnu da kanta, sai mu ka ga screen din ya nuna "searching... Sai abokina ya yi murmushi ya ce "yawwa ta kunnu😁. Da ma wayar tana hannuna, ba a yi minti 2 ba sai rubutun ya 6ace wani ya fito. Tracking.. Tracking... Tracking kawai ta ke nunawa🙄 Ina ganin haka sai na miqa Masa wayarsa, Amma sai ya Yi kamar bai ga Ina miqo Masa ba. Sai na ce Masa "amshi wayarka!". Wai sai ya ce min "ba hannunka take ba, ka riqe ta har ta gama tracking din ta Mana"🙄. Na ce Masa "tayi tracking din mi🙄? Malam dalla riqe wayarka". Sai ya ce "haba bar ta wajenka har ta gama tracking din network dinta, ba Ina Nan ba,ko guduwa zan Yi ne?🙄". Na ce "Kai Malam amshi wayarka ta Yi tracking din network din a hannunka, na tura Masa ita cikin aljihu na Yi gaba na bar shi baya.

Ha'a! Kawai ba sai na ga abokina ya wuce ni a sukwane ba🤔 ai Nima sai na bishi a dubu, da na taddo shi muna gudu na ce Masa gudun me mu ke? Sai ya ce ai wayar ce ta rubuta LOCATION FOUND 😯😮watau ko su waye sun Gane haqiqanin wajen da wayar ta ke! Kam ai sai na qara giya, Ina gudu na juyo sai na ga abokina na bina Shima a dubu Kuma ga wayar a hannun shi, ai sai na qara wuta, da dai na ga ya liqe man bumpa to bumpa sai na yanke na fada daji da gudu. Na Yi gudu ya Kai na minti 5 ina tunanin na 6ace Masa kawai sai na hango shi ya shawo kwana da gudu ya nufo inda Nike da Wayar a hannunsa😮 Kam bala'in nan! Gudu bai qare ba kenan. Ai sai muka qara retawa a guje
🏃🏃
Ko yanxu haka Ina gudu Ina rubuta wannan post din, Kuma shi Dan shegiyar ya qi daina bi na, ga shi Kuma ya kasa yadda wayar sai ka ce uwarsa ce ta Zama iPhone din, ya wani maqalqale ta, ko da ya ke ban ga laihinsa ba, Dubu Hansin ai ba Wasa ba ce.

©️ Yusuf Rabiu Jibia™️
Post a Comment (0)