Ɗan Uwa in dai ba ka auri mai Addini ba sunanka 'Sorry'.
'Yar Uwa in dai ba ki auri mai Addini ba sunanki 'Sorry'.
Mai Addini ita ce mai tsoron Allah.
Idam ba za ka iya leƙa zuciyarta ba; za ka gani a biyayyarta ga umarninShi!
Mai Addini shi ne mai tsoron Allah.
Idam ba za ki iya leƙa zuciyarshi ba; za ki gani a biyayyarshi ga umarninShi!
Ba da yawan karatu ake gane mai Addini ba... Domin da Karatu ne da Abduljabbar ɗan Nasiru Kabara da Bil'amu ɗan Ba'uura sun kasance nagartattu 📌
Sai da shi Ilimi yana mai da ma'abocinshi tamkar Ɗawisu a cikin sauran tsuntsaye. Ko kuma lu'u-lu'u cikin albarkatun ƙasa.
Game da Ilimi; Abbammu (Allah ya jikanshi da rahmah) yana yawan ba mu misali da maganar Shehin Musulunci Ibn Taimiyyah (R) cewa:
"Shi Ilimi tamkar ruwan sama yake. Ya danganta da bishiyar da ya sauka. In ta 'ya'yan marmari ce sai tai kyan gani. 'Ya'yanta su ƙara zaƙi. Idan mai ɗaci ce. Sai tai shar. Ta yi ɗaci sosai".
Maza kyau abun lura ne. Amma ba shi ne muhimmi ba. Mata dukiya abar lura ce; sai dai ba ita ce mafi mahimmanci ba.
Allah ya sa mu dace. Don rahamarShi; ba don halimmu ba 🤲🏽
✍🏼- Muhammad Abuzar