MUSULUNCI YA FARA NE YANA BAƘO

MUSULUNCI YA FARA NE YANA BAƘO






Sahabi Abu Huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce:
 بَدَأَ الإسْلامُ غَرِيبًا، وَسَيَعُودُ كما بَدَأَ غَرِيبًا، فَطُوبى لِلْغُرَباءِ.
"Musulunci ya fara ne yana baƙo, da sannu zai koma baƙo kamar yadda ya faro,, madallah da baƙi"
صحيح مسلم (١٤٥) •
Imam Laith bn Sa'ad yana cewa:
"من لم يشعر بالغربة فليس على السنة"
"Duk wanda baya jin baƙunta baya kan Sunnah ne"
ذم الكلام.

Waɗannan ruwayoyin suna bayyana mana yadda addini ya fara ana kallon ma'abotansa sun kawo wani sabon baƙon abu, saboda sun saɓawa abinda aka tashi aka gani iyaye da kakanni, to kamar haka a ƙarshen zamani idan mutane suka koma yin addini yadda suka tashi suka ga ana yi ba hujja ba dalili, sai aka samu waɗanda suka ce lallai sai anyi addini irin yadda yazo a lokacin baƙunci, suma sai su zama ana musu kallon sun kawo baƙin lamura, amma a ƙarshe idan suka jure su ne da ribar aljannah.

Allah yasa mu dace.
Post a Comment (0)