Addu'o'i yayin jin kiran Sallah

Addu'o'i yayin jin kiran Sallah 







Wanda ya ji kiran salla zai faɗi dukkan abin da ladanin yake faɗi, sai dai idan ya ce: 

حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ da وَحَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ
 Fassara:
Ku taho ga salla; Ku taho ga babban rabo. maimakon haka sai shi ya ce: 

لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ
 Fassara: 
Babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah. 




Bayan ladanin ya yi kalmar shahada, sai shi (mai sauraron) kuma ya ce:

وَأَنَا أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا.

 Fassara: 
Ni ma ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kaɗai, babu abokin tarayya a gare Shi, kuma Muhammadu bawansa ne, kuma manzonsa ne. Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne Addini. 
 
Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. 




Sannan ya ce:

اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلَاةِ الْقَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدًا الْوَسِيلَةَ وَالْفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامًا مَحَمُودًا الَّذِي وَعَدْتَهُ، [إِنَّكَ لَا تُخْلِفُ المِيعَدِ]. 
 Fassara: 
Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita, Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma Ka tashe shi a matsayi abin godewa¹, wannan wanda Ka yi masa alƙawarinsa. Lalle Kai ba Ka saɓa alƙawari.

Sannan ya yi wa kansa addu’a tsakanin kiran salla da tayar da iƙama, domin addu’a a wannan lokaci ba a ƙin karɓar ta..

#Zauranmukarudajuna 

 Whatsapp chanel 👇 
https://whatsapp.com/channel/0029VaAK7QU2phHT5pjZPI12

 Telegram
Post a Comment (0)