WaΖ™ar So






Tun Tsuntsaye su na sheΖ™a
Dukkan Sassa Na LelleΖ™a
Don warware Ι—aurika sarΖ™a
Da su kai wa rai riΖ™on Salka
      A Sahara ba Sakaina ba

So ya yi min riΖ™on Sanda
Ta Makaho mai tsayin wada
Na tadda ruwa cikin Randa
Ga Ƙadangaruwa ta na raΙ—a
      Ba ta barni na je ga ma'un ba

Kin kyasta wuta cikin raina
Kin sawa dukan jiki Ζ™una
Ya zan na ciko muradina?
Don cimma biΙ—a ta Ruhina
      Ba zan kaico na kasa ba

Kin zamo kwaΙ—on jikin carbi
In ba ke yanzu wa zan bi?
Mai kyan zane kamar Zabi
A cikin raina akwai gurbi
     Ga watarki ba shi dace ba

Kin zam a garan kamar riga
Ko gun mai Rijiya Guga
Ya tilo mai kamar zuga
BuΙ—e Ζ™ofarki in dirga
      Na san ba zan nadama ba

Magaji Kabiru Getso
Post a Comment (0)