*Tambaya*
Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa ?
*Amsa*
Wa'alaikum salam,
To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za'a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa: babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba'a yi masa kaciyar ba, daga cikin ka'aidojin malamai shine duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dan karami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7 \ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349
*Dr. Jamilu Zarewa*
18/11/2014
*ZAUREN📚DARUL-ISLAM📚*