NA JONA SALLATA DA TA MAMU BAYAN AN GAMA SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?

NA JONA SALLATA DA TA MAMU BAYAN AN GAMA
SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?

Tambaya:​

Assalamu alaikum malam. Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam'i
ba sallah? Misali, na zo masallaci na taradda jam'i na sallar
asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don karasa raka'a
2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada jam'i da ni.
Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya halatta, tare da
hujjoji.

Amsa​

Wa alaikum assalam.To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar
zuwa zantuka guda biyu:

1. Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin
hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba, sannan kuma
shi masabuki ba liman ba ne, Annabi S.A.W kuma ya yi umarni
da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta
ki karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in ya gama
yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka sai ya
haramta . Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma Mawahibul-jalil
4\489.

2. Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin
zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu
Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da daddare sai ya
bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba
ta:666, A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya halatta
mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi
niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi S.A.W bai hana
Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara da
shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da
liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai ne, don
haka sai ya halatta a bi shi.
Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.

Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu saboda abin da ya
gabata da kuma hadisan da suke nuna falalar sallar jam'i.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07/12/2014

Post a Comment (0)