SHIMFIDAR MATAR AURE

SHIMFIƊAR
MATAR AURE
        ___
        🧕🏻


         
1. 
Shimfiɗar fuska itace wadda ta fi shimfiɗar tabarma:

Ba domin an shimfida maki dukiya da ilmi a rayuwar ki ba, shine yake nufin an miki gatan gidan miji ba. Sannan ba kuma yawan kayan ɗaki da kyan sifa ke zaman aure ba, baicin *Nagarta*

Idan kika nagartu;
a sannan ne ilimin, dukiyar da kyawon sifa zasu haɗu su mai dake; *"Tsadaddiya"*

Da komai kyanki nasabar ki, dukiyar ki, da ilimin ki; a banza ne idan kika kasa:

Biyayyar aure
Sadaukarwa
Yi nayi - bari na bari
Gyara, tsabta, kwalliya
Hakuri, juriya, yafiya
Kauda kai, da sakewa

Domin da dukkaninsu ne ake sarrafa so da kauna har ki zamto nutsuwa, da shine sahalar matar aure:

Da idan kika kasa aiwatar da wa'yannan !? Da kuma dukkan dalilan da ake auren mace a dalilin su, ai basu amfane ki ba, domin:

Ba dukiya, sarauta, kyan sifa da ilimi bane kaɗai ake tinƙaho ba; sai ki kin shimfiɗa su a gidan aure a aikacen ki da lafuzzan ki, har ki zamto mai ƙima a idon mijin ki da 'yan uwan sa da jama'ar da kika mu'amalanta:

Don da wannan ƙimarce ake kimanta ki, da 'yayan ki, da 'yan uwan ki da darajar gidan ku, har a martabaku a baku lambar yabo:

Abinda hakan yake nufi !? 
Ki sadaukar da kan ki, zuciyar ki da sassan jikin ki dan ki zamto ga mijin da igiyoyin auranki 'yancin ki da aljannar ki suke ƙarkashin ikon sa; salihar mace mai wanzar da nutsuwa a gare shi !? 

Da yake nufin baza ki aiwatar ba sai abinda aka umarce ki, kuma ki kyautata aiwatarwar yadda zaki burge shi:

Haka kuma zaki nisanci ababen da duk ya hana ki da zuciyar ki da sassan jikin ki, ya zamto koh a bayan idon sa baza ki aiwatar ba, sannan baza ki rika mita akan hanin da aka miki ba balantana kiyi fushi :

Sannan ki kyautata da dukkan abinda sunan shi kyautatawa ne, kuma kyautatawar ta zamto da ƙarfin ki da dukiyar ki da lokacinki; tsakanin farin cikin ki da bakin cikin ki ba don ki goranta wata rana ba:

Tsakanin bin umarnin Allah da hanin Sa, domin babu ɗa'a ga abokin halitta domin a saɓawa Mahalicci. 

👌🏼 Ku biyo ni bayan post na biyun shi.

               🛡️
Health Talk 4 Both
+2349077562389
Edited on: 22/9/20
Post a Comment (0)