Assalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,109
.
Wata matace, ta haihu ne to tayi wajan 2 month period nata baidawo ba sai randa aka dau axumi taga wani abu mai yauki kaman majina amman yana hadeda jini sai dai jini ba ja sosai bane kuma baya karni sanna kuma yayita zuwa ne kaman majina har tswon kwana uku to yanxu wannan kam zata biya azumin ne sanna kuma intaxo yin wanka wani irin niyya zatayi??
.
.
.
Amsa
.
..
To wannan tambayar akwai wani abu acikinta, abun kuwa shine akwai buqatar musani shin sadda ta haihun taga jini kokuwa bata ganiba?? Idan taga jini sai jinin ya dauke shine bayan daukewarshin har watanni biyu bataga al'adarta ba, sai bayan watanni biyun taga wannan kalarda tace tagani?? To idan haka take nufi, to inhar tana iya gane kalar jinin hailarta saita duba tagani, inhar wannan ruwan shine irin jinin hailarda tasaba gani dama aduk lokacin hailar, to shikenan wannan din datagani yanzu to hailace dan haka bayan sallah zata rama azumin wayannan kwanakin sannan kuma niyyar wankan haila xata yi.
Inkuwa sanda ta haihun kwata kwata bataga jiniba sai wannan wanda tace taganshi a bayan watannin biyun to shima dai hukuncin iri dayane da bayaninda mukayi asama
Amma dan wannan ruwan bashine irin jinin hailarda tasabayi ba, to anan zata bashi hukuncin damu fasadinne wato jinij ciwo, kenan azuminta na wayannan kwanakin sunyi, sannan kuma babu wankanda zatayi sedai wanka na tsafta da jin dadi
Inkuma wannan kalar da ta gani yazo matane kafin ta cika kwanaki 40 ko 60 da haihuwa shine taga wannan kalar ruwan to anan kuma jinin haihuwane dan haka batada azumin wayannan kwanakin, sannan kuma wankan da zatayi shine na yankewar jinin haihuwa
…
…
.
Allah yasa mudace
.
.
.
DAGA ZAUREN
.
SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM
.
Watsaps
08161884309
.
.
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika