MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA???
Assalamu Alaikum warahmatullah. Mallam dan Allah meye hukuncin wanda ya kwana da maniyi a jikinsa kuma yayi sallah amma yayi tsarki irin na fitsari?
الحمد لله رب العالمين.
Amsa: Wa'alaikumus salam warahmatullah wabarakatuhu, idan dai kana nufin kayi sallah alhali kasan kana da janabah, to abune sananne a wajan musulmi cewa tsarkin hadasi babba ko karami, wajibine, kuma sharadine na ingancin sallah, duk wanda yai sallah bashi da tsarki da gangan koda mantuwa sallarsa batacciyace bataiba, saiya sake, idan daganganci yayi hakika ya aikata babban laifi cikin manyan laifuka dakuma zunubi mai girma.
Shaikul islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace:
"Musulmi kada yayi sallah a inda ba alkibla bane, kada yayi sallah batare da alwala ko ruku'u ko sujjada ba, wanda ya aikata haka yacancanci zargi da uquba,
Min hajussunnah (5/204).
Hakika gargadi mai tsanani yazo gawanda ya aikata haka;
Hadisi daka Abdullahi dan mas'ud yardar Allah takara tabbata agareshi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: (Anyi Umarni ayiwa wani bawa daka cikin bayin Allah bulala dari acikin kabarinsa, bai gusheba yana tambayar dalilin bulalar dakuma rokon asassauta masa harsaida ya rage saura bulala daya, sai aka karasa masa dayar, aka cika kabarinsa da wuta, lokacin da'aka dauke masa azabar bayan yafarfado sai yace kusanar dani sabo dame akaimin bulala? sai akace dashi kayi sallah ne sau daya batare da tsarki ba, kawuce tawajan azzalumi kuma baka taimakeshiba) Addahawi yaruwaitoshi acikin mushkilil Ãàsaar Albani ya hassanashi acikin silsila saheeha (2774).
Malamai sunyu ittifaqi akan duk wanda yai sallah batare da tsarki ba yana mai halatta hakan, ko saboda isgili, hakika yakafirta, za'a nemi yatuba, idan bai tubaba za'a kasheshi.
Amma idan mutum yai sallah batare da alwala kawai dan wulakanta sallah, bai halatta hakan ba kuma ba izgili yakeba, Imamu Ahmad yatafi akan cewa mutum yakafirta, jamhurdin malamai kuma sukace: bai kafirta ba, saidai abunda yayi babban laifine cikin manyan laifuka.
Imamun nawawi rahimahulla yace:
Idan mutum yasan yanada hadasi kuma yasan sallah ba tsarki haramunne, abunda yayi laifine babba cikin manyan laifuka, baya kafirta awajanmu, saidai idan yahalatta sallah batsarki ne, Abu hanifa yace yakafirta saboda izgilinsa.
Abunda yake wajibi akan wanda yai sallah babu tsarki shine yatuba, yayi istigfari, yakuma kuduri niyyar bazai sake aikata hakan ba, sannan saiya sake sallar daya sallata batare da alwala ba, Allah madaukakin sarki yana karbar tuban wanda yatuba yakoma gareshi. Haka kuma irin wannan bayanin naka koda ace janabar ta same ka ne da dare sai kaji baka iya yin wanka a lokacin kayi alwala ka kwanta, to dole ne idan ka tashi kafin kayi sallar asubah sai kayi wanka sa'annan kayi sallah. Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin Musulunci
Whatsapp group