ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN DADIRO DA ITA?

ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN DADIRO DA ITA?

                            Tambaya:
As SALAMUN alaikum, Malamai ya halarta musulmi ya musuluntar da matar da yayi zaman daduro da ita bayan hakan ya aure ta, limanmin da ya goyi bayan hakan yayi daide? Please is very important"
 

                               Amsa:
Wa'alaikum as salam, ya halatta sabida babu alaka tsakanin dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun tuba, saboda musulunci yana rusa abin da ya gabace shi na zunubi kamar yadda ya tabbata a hadisin Amru bn Al'ass.

Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah yana gafarta dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda aya ta:53 a suratu Zumar ta tabbatar hakan
 
Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa 

1\2\2016.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)