MIJIN DA KE NUNA BANBANCI A TSAKANIN MATAN SA

TAMBAYA TA 029

Assalamu alaikum, Dan Allah Ina da tambaya. Mata Ce su biyu wurin mijinsu.  Uwargidan na da Yaya Goma ita kuma Amarya na da biyu.Duk dawainiyar Uwargida da yayanta Shi Ya ke yi Har da Kudin makaranta Boko da Arabiya.Amma Ita Amarya ya bar mata lamarin ta da na taunts Ko kudin makaranta ba Ya Biyan Ma yaranta.Ta yi Korafi duk abanza Sai dai alkwarin da baya cikawa.Gidan da su ke zama na yan uwan Amarya ne sabida Haka Ko kudin haya ba Ya biya shekara uku kenan Ko NEPA sun kawo bill Sai dai amaryan ta biya kuma na Wai Baida Shi ba ne Don Shi Ya ke daukan dawainiyar Gidan Uwargidan shi.Amaryan na Sanaar siyar da atamfofi last year azumi ya daukan Ma matar sa da mahaifiyarsa, yaransa da abokanan Huldan sa kaya Har na Kimanin dubu Dari da Talatin Amma bai yi MaNi yarinyar amaryan Kayan sallah  ba.
Toh Har yanzu Ya ki Biyan kudin.To saboda da addini ya Ce da matar da kudinta duk suna karkashin sa ne. Za ta iya dage wa Sai Ya biya ta kudin ta don ita ke daukar dawainiyar yaranta, Suturan su da kuma kudin makaranta su.Don Allah a Taimaka da amsa a addinance. Na gode

AMSA
W alkm slm w rhmt Laah.

Da farko dai ina son yin nasiha ga masu rubutu da su rika kulawa da ka'idojin yadda ake rubuta wadansu abubuwa, kamar kalmar: 'don Allaah' da harafin 'o' ne, ba da harafin 'a', watau 'Dan Allaah' ba! Domin wannan ta karshen tana iya sa a yi masa mummunan fassara. Allaah ya shiryar da mu.

Amma game da wannan tambayar, Allaah Madaukakin Sarki ya ce:
وعلى المولود له رزقهن وكسوتهن بالمعروف
Wajibi ne a kan mahaifi ya ciyar kuma ya tufatar da uwa da danta, a bisa ka'idar da aka sani a Shari'a.

Sannan kuma Annabi (Sallal Laah Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi magana a kan haqqoqin mace a kan mijinta, ya ce:
أن تطعمها إذا طعمت، وتكسوها إذا اكتسيت، ولا تضرب الوجه، ولا تقبح، ولا تهجر إلا في البيت.
Ka ciyar da ita idan ka ci, ka tufatas da ita idan ka tufatu, kar ka bugi fuska, kuma kar ka yi zagi, kuma kar ka kaurace sai a cikin daki.

Haka kuma ya fada a cikin wani hadisin ya ce:
كفى بالمرء إثما أن يضيع من يقوت.
Ya ishi laifi ga mutum ya tozarta wanda yake ciyar da shi.

Daga wadannan nassoshi sahihai ya bayyana a fili cewa, daga zaran an daura wa mace aure da miji kuma har ta tare a gidansa, to haqqinsa ne ya ciyar da ita, ya tufatas da ita da gwargwadon karfinsa da ikonsa. Kamar yadda ya wajaba a kansa ya ciyar kuma ya tufatas da 'ya'yan da ta haifa masa.

Duk yadda mace take da dukiya a karkashin mijinta ba haqqinta ne ta ciyar da kanta ko 'ya 'yanta ba, sai dai ta fuskar kyautatawa ga shi mijin, ko kuma in akwai wata yarjejeniya a tsakanin su da ta hukunta hakan run farko.

Sannan kuma duk namijin da Allaah ya hore masa har ya sami hali ko ikon auren mata fiye da daya har zuwa hudu to daidai ne, kuma abu ne mai kyau, kuma yana da lada mai yawa, in sha'al Laah. Amma kuma dole ne ya san cewa Shari'a ta halatta masa yin karin aure ne kawai a kan sharadin zai iya yin adalci a tsakanin dukkan matansa.

A duk lokacin da namiji ya san cewa ba zai iya yin adalci a tsakanin matansa ta fuskar ciyarwa da shayarwa da tufataswa da rabon kwana da makamantan irin wadannan abubuwan na fili karara ba, to bai halatta ya kara auren ba.

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
من كان له امرأتان، فمال إلى إحداهما دون الأخرى، يأتي يوم القيامة وشقه مائل.
Duk wanda yake da matan aure guda biyu, sai kuma ya karkata ga guda daya daga cikinsu ya kyale gudar, to zai zo ranar Kiyamah sashen jikinsa ya shanye!

Saboda haka, abin da ya kamaci wannan matar da take fuskantar wadannan matsalolin da ta yi bayani daga mijinta shi ne:

Ta cigaba da yin hakuri, da jawo hankalinsa cikin hikima ga irin wadannan nassoshin da suka gabata a sama. Mai yiwuwa Allaah ya ganar da shi, har ya dawo kan hanya. Allaah ya taimake mu.

Idan kuma hakan ba ta biya bukata ba, to a Shari' a ba laifi ba ne idan ta dauki maganar ta kai gaban wani alkalin kotun musulunci domin neman ya fitar mata da haqqinta.

Sai dai wannan din yana da girma sosai. Don haka ta tsaya tukun ta yi tunani sosai kuma ta yi shawara da iyayenta da amintattun masu hankali a cikin makusantanta kafin ta dauki wannan matakin na karshe.

Wal Laahu A'lam.

Amsawa: Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Daga: Majlisin sunnah
www.facebook.com/majlisinsunnah

whatsapp  +2348164363661

Post a Comment (0)