TAMBAYA TA 008
Assalamu alaikum
Malam Macen da mijinta ya sake ta tana da karamin ciki bayan sun rabu sai tayi barin cikin
Ya idda ta take akansa
Akwai iddar sa akanta ko babu?
AMSA
Daga nassin Alqur'ani (surah at-talaaq: 3): 'Kuma masu cikunna, karshen iddarsu ita ce su sauke cikinsu.'
Sannan a cikin hadisin Subai'atul Aslamiyyah wacce ta haihu bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, kuma ta tambayi Annabi (sallal Laahu alaihi was alihi wa sallam) a kan maganar iddarta, ta ce:
'Sai ya ba ni fatawa da cewa, na gama iddata a lokacin da na haihu, kuma ya umurce ni da in yi aure a lokacin idan ina bukata.' (Al-Bukhariy da Muslim suka fitar da shi).
Saboda gamammiyar maganar da ta zo a cikin wannan hadisin ba tare da ya nemi sanin irin abin da ta haifa ba, sai malamai suka ce:
'Iddar mai ciki yana kammaluwa da zaran ta haihu, kuma ko da abin da ta haifa da daya ne ko tagwaye, kuma mai cikakken halitta ne ko a'a, kuma rayayye ne ko matacce, haka ko gudan tsokar nama ne ko gudan jini ne kafin ya zama jariri. (An-Nawawiy a cikin Sharhu Muslim).
Sannan kuma Ibn Al-Munzir a cikin (Al-Ijmaa'u) ya ce:
'Duk malaman da muka dauki ilimi daga gare su sun yi ijma'i a kan cewa, iddar mace yana cika idan ta yi barin abin da aka san cewa da ne.'
Wal Laahu A'lam.
Amsawa: Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Majlisin sunnah
www.facebook.com/majlisinsunnah
whatsapp +2348164363661
Instagram: muneerassalafy
E-mail: massalafy8@gmail.com