YAUSHE AKE YIWA YARO KACIYA ?
Tambaya
Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa ?
Amsa
Wa alaikumus salam,
To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za'a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa : babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba'a yi masa kaciyar ba, daga cikin ka'aidojin malamai shi ne duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dankarami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7\ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.
Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
30/09/2016