WAJABCIN YIN WANKA BAYAN FITAR MANIYYI

_*Wajibcin Yin Wanka Bayan Fitar Maniyyi.*_

_*Tambaya:*_

Assalamu Alaikum warahmatullah

Dan Allah malam inna Neman karin ilimine akan Matan da ta wetting kanta tana bukatan tayi wankan starki ko kuwa basai tayiba?

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah Wabaratuhu._

_Ƴar uwa wajibi ne ga mutum Musulmi namiji ko mace ya yi wanka yayin da *Maniyyi* ya fita daga jikinsa ta hanyar jindadi ko a cikin barci._

_Domin *Allah (ﷻ)* Ya ce:_

_*”....وَإِن كُنتُم جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا....“*_

_Ma'ana: *“Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi tsarki (wanka)”*   (Alma’ida : 6)._

_Kuma *manzon Allah (ﷺ)* ya faɗi ga Aliyu cewa: *“Idan ka fitar da ruwa (Maniyyi) to ka yi wanka”* [Abu Dawud ne ya rawaito shi]._

_Sannan kuma an karbo hadisi daga Abi Sa'idul khudry (r.a) ya ce: *manzon Allah (ﷺ)* ya ce: *“Wanka yana kasancewa saboda fitar Maniyyi”.* Muslim ya ruwaito shi, amma asalinsa a cikin Ɓukhary ne._

_Saboda haka ƴar uwa duk wadda ta yi *wetting* ɗin kanta, to wajibi ne akanta ta ti wanka._

_Allah Ya bamu ilimi mai amfani👏🏽._

_Amsawa: *Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*08166650256.*_

_Daga Zauren:_

_*🧕Islamic Post Women.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._

1 Comments

Post a Comment