WANENE BA ZAI GA ANNABI SAW BA A RANAR ALKIYAMA?

WANE NE BA ZAI GA ANNABI (S.A.W) BA A RANAR KIYAMA?

Daga Nana Aisha (ra) tace: "Na kasance a cikin dakina ina dinke wani tufafi nawa sai fitila ta mutu kuma dakin ya yi duhu
lokacin da alluran ta fadi kasa, ina cikin wannan hali ina laluben alluran sai ga Manzon Allah (SAW) ya bullo da fuskarsa daga kofar daki. "Ya daga labulen kofar sannan ya shigo da fuskarsa".

Nana A'isha tace "Na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi
hakika sassan dakin ya haskaka daga hasken fuskarsa.

Sai na waigo zuwa gare shi
nace Mahaifina fansa ne a gareka ya Manzon Allah BABU ABIN DA YAKAI FUSKARKA HASKE!
Sai Annabi (SAW) ya ce: "ya A'isha, kwarin azaba ya tabbata ga wanda ba zai gan ni
ba ranar alkiyama!"

Sai Nana A'isha (RA) tace: "Wanene ba zai ganka ranar alkiyama ba, Ya Manzon Allah?
Ta maimaita sau biyu.

Sai Annabi (SAW) ya ce: "wanda aka ambace ni a gurinsa bai yi salati a gare ni ba."

SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM.

TIRMIDHI Da IMAM AHMAD

Dan Allah idan ka karanta kayi sharing koda a group 10 ne domin yan uwa sugani su amfana.

Post a Comment (0)