SHIN MACE MA ZATA BAYYANA KARATU A SALLAH?

_____TAMBAYA __  Malam shin mace itama  zata bayyana karatun sallah a sallolin Magriba,Isha'i,Asubahi da Qiyamul laili?                              _____ Amsa ____        Manzon Allah (s a w) ya ce: "صلو كما ،رأيتمونى اصلى (kuyi sallah kamar yadda kuka gani ina yi)".          Annabi (s a w) yayi umarni da yin sallah yadda yake yi ba tare da kebance maza ko tsame mata ba.Mace da namiji duk iri daya zasu yi.                    Sai dai malamai sun yi bayani cewa mace bazata daga murya sosai ba lokacin da take karatun sallah ,za tayi ne yanda zata jiyar da kanta da kuma na kusa da ita.                'Yan uwa mata da yawa kan yi karatun sallah kowacce a boye wanda yin hakan kuskure ne.               Allah ya bamu ikon gyarawa ameen. ka turawa 'yan uwa dan samun ladan bayyana ilimi.

Post a Comment (0)