HUKUNCIN WANDA YA FITAR DA MANIYYI SANADIYYAR FIRGITA KO AZABA

*HUKUNCIN WANDA YA FITAR DA MANIYYI SANADIYAR FIRGITA KO AZABA*

*TAMBAYA*
Assalamu alaikum
Malam, Dan Allah inada tambayoyi kaman haka Dan Allah Malam.
1)  Ni ne idan naga wani abin ban tsoro ko na razana sai wani ruwa yana fitowa kaman maniyyi. Me wannan abun, kuma hukuncin wanka ya kamani ko dai❓
2) Sai tambaya na biyu
Nayi rashin lafiya ne da ban san ma inda nake ba, sai ya zama ban yi sallah na kwana biyu ba. Idan zan rama ya zan yi malam❓

*AMSA*
Wa alaikumus salamu warahmatullah.

✔1). Idan mutun ya razana har yafitar da miniyyi, wannan ba janaba bace, wankan janaba yana kamawa ne da fitar maniyyi da jin dadi abun sabawa acikin bacci ko a farke da jima'i ko waninsa,
Na biyu boyon kan kaciya acikin farjin mutun ko ta dabba.
Kamar Hadisin Ummu Sulaim da tayi tanbaya akan macen da tayi mafarkin ana jima'i da ita, shin zata yi wanka❓
Sai yace:( *EH, AMMA IDAN TAGA RUWA*).
👉Buhari:282.📗
👉 Muslim:313.📘
Wani mutun kuma yayi mafarkin yana jima'i da mace, amma baiga ruwa ba, bayan ya tashi, sai Annabi _Sallallahu alaihi wasallam_ yace:( *BABU WANKA AKANSA*).
👉 Tirmiziy:113.📓
👉 Abu dawud:233.📚
Daga Aisha Allah yakara mata yarda.

Misalin na biyun :
Annabi _Sallallahu alaihi wasallam_ yace ma wanda yayi jima'i ( *WANKA YA WAJABA AKANSA KODA BAI FITAR DA MINIYYI BA*).
👉 Muslim:348.📕

Daga Abu Hurairah _Allah yakara masa yarda_
Wadannan ababen kawai kesa wankan janaba,
Amma da mutun zai dauki kaya masu nauyi, ko ya fada wuta, ko yasha dan karen duka, ko kunama ta harbi azzakarinsa, da dai sauransu, har maniyyi ya fita saboda azaba, to babu wanka akabsa saboda ba da jin dadi yafito ba,
Kamar mai Mukhtasar yayi wannan bayanin.
✔2). Zaka rama sallar ne ajere yadda tazo, zakayi azahar daya sai kayi la'asar daya, sai kayi Magriba daya, sai kayi Isha'i daya sai kayi Asuba daya haka har kagama, domin jerantawa dole ne yadda sallolin sukazo,
Idan wadda ake bayyanawa ce zaka bayyana koda da rana zakayita, wadda ake boye karatunta kuma zaka boye koda da daddate zakayita.
Sabida lokacinda Annabi bai samu yin Sallar la asar cikin lokaciba har Rana ta fada sai yaje Rafin Buduhan yayi alwallah sannan yadawo yayi LA asar tukun kana yayi Magrib.
👉Buhari:597,598.📗
👉Muslim:209. 📘
Misalin na biyun :
Lokacinda Annabi yayi bacci bai samu yin Sallar Asubaba har rana tafito yayita ne yadda yasaba yinta cikin lokaci ko mai da komai kuma rana ta fito ya bayyana Asubar da natsuwar da dai sauransu.
👉Muslim:680.📓

*Tsokaci:*
Bai halatta ajinkirta Sallah domin rashin tsarki ko rashin Lafiya, indai mutun na cikin Hankalinsa, to dole yayi sallah acikin lokacin koda ba alwallah ba taimama ba fuskantar Alkiblah Gwargwadin iko.

👇👇👇👇👇👇👇👇
والله تعالى أعلم
〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰
✏ _AMSAWA_:🖊
*SHAFI'U SHEHU MINNA*✍
(☎ *08033410797*)
daga zauren:
*_ISLAMIC GROUP 1 & 2_*🌙
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼

Post a Comment (0)