SHIN MAI SALLAR FARILLA ZAI IYA BIN MAI SALLAR NAFILA?

*_SHIN MAI SALLAR FARILLA ZAI IYA BIN MAI SALLAR NAFILA?_*

                                 *Tambaya*
Assalamu alaikum, malam maye hukuncin mai bin sallar farilla ga me nafila, Malam Allah ya kara lafiya, ya ja kwana.

                                     *Amsa:*
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar, saidai zance mafi inganci shi ne hallacin hakan, saboda Mu'az dan Jabal R.A ya kasance yana yin sallar Isha tare da Annabi ﷺ sannan ya je wajan mutanensa ya jagorance su sallar isha, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 711.

Malamai suna cewa: daya daga cikin sallolin Mua'az a nan nafila ce, tun da ba'a yin sallar Isha guda biyu, don haka ko dai ya zama wacce ya yi da Annabi ﷺ ita ce nafila, sai ya zama ya yi koyi da mai farilla, ko kuma wacce ya yi da mutannansa ita ce nafila, don haka sai ya zama mutanansa suna farilla, shi kuma yana nafila, a kowanne daya daga cikin biyu, zai zama akwai inda mai nafila ya yi koyi da mai farilla.

Kasancewar an yi abin a zamanin Annabi ﷺ bai yi inkari ba, dalili ne da yake nuna ingancin hakan, tun da ba ya yin shiru idan ya ga kuskure.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani duba: Almajmu'u na Nawawy 4\169.

17\2\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)