YANA DAGA CIKAR TAUHIDI WADATUWA DAGA MUTANE?

*_YANA DAGA CIKAR TAUHIDI, WADATUWA DAGA MUTANE???_*

                               *Tambaya:*
Assalamu Alaikum Malam Dan Allah ka warwaremin wannan mas'alar. Lokacin da aka jefa annabi Ibrahim a wuta kamar yadda ake cewa mala'ika jibreel ya Zo masa yace Ze tamakeshi shiko yace : temakon Allah yake nema, har ya fadi abin da ya fada na hasbiyallahu wani'imal wakeel se Allah yace yaanaru kuniy bardan wasalaman alaa Ibrahim.
Toh inda ishkalin yake shi ne tabbas mala'ika da temakon Allah xe temakeshi Amma yace bayaso., yanxu wannan yana nuna cewa be halasta mutum yayi addu'a Akan Allah ya daura shi Akan wane yasamu wani Abu da yake nema wurinsa ba, sawaa'un kudi ne ko wani Abu ba. Sedae kawai yai ta addua dacewar Allah ka temakeni da niyyar cewa shi Allah in ya tashi ya san ta ina ze temake shi ?

                                     *Amsa*
Wa'alaikum assalam To dan'uwa kissar Annabi Ibrahim da Mala'ika Jibrilu tana daga cikin labaran da aka samu a litattafan Yahudawa da nasara, Imamul Bagawy ya yi nuni zuwa ga rauninta a tafsirinsa, haka nan Albani a Silsilatu Adda'ifa 1\74, in da ya siffanta kissar da cewa ba ta da asali.

Ya halatta mutum ya nemi taimako a wajan wani, saboda fadin Annabi s.a.w. "Roko ba ya halatta sai ga mutum uku : daga ciki akwai wanda yau ta kama shi ya rasa abin rayuwarsa za ta gudana da shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1044.

Saidai yana daga cikin cikar imani kada mutum ya nemi taimako a wajan kowa,  in ba Allah ba, Annabi ﷺ ya yi alkawari da wasu sahabbansa cewa: ba za su tambayi kowa wani abu ba, wannan ya sa ko da bulalar daya daga cikinsu ta fado yana  kan abin hawansa ba zai ce wani ya miko masa ba, saidai ya sauko ya dauka, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1043.

Annabi ﷺ ya yi bayani cewa akwai mutum 70,000 da za su shiga aljanna ba tare da hisabi ba daga cikin siffofinsu akwai rashin neman wani ya yi musu addu'a in cuta ta same su, kawai da Allah suke dogara, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 6175.

Allah ne mafi sani.

19\2\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)