SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCIN SU

*_SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU_*

                                  *Tambaya*
Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan "KUDRA da kuma SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.

                                      *Amsa*
To 'yar'uwa, Wannan yana daga cikin mas'aloli masu mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwaka game da hakan: Sufra na nufin mace  ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan ciwo, ya fito daga gabanta.

Kudra kuwa na nufin: ruwa ya ringa fitowa daga farjin mace, wanda kalarsa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da baki wato kamar ruwa gurbatacce, Dangane da hukuncinsu kuwa: idan daya daga cikinsu ya  kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan kuma bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fadin Ummu adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra bayan tsarki a  cikin haila) Abudawud ya rawaito shi da sanadi mai inganci.

A hadisin A'isha kuma (Mata suna aiko mata da abin da suke sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, ta yadda za mu yi amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki, ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila ba, hadisin A'isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana cikin haila ta yadda za ta kirga da su.

Don neman karin bayani duba: Dima'uddabi'iy a shafi na: 8.

Allah ne mafi Sani.

6/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)