TA AKE YIN WANKAN JANABA DA HAILA?

_Assalamu alaikum
Warahmatullah._

_*Tambaya:*_

Ya a ke yin wankan haila da na janaba?

_*Amsa*_

 'Yar uwa! Wankan haila da na janaba duk iri daya ne, bambancin Niyya ne kawai.

Yanda ake yi shi ne: Dafarko za ki kudurta a zuciyarki kalar Wankan da za ki yi, wato Niyya (Kamar Wankan Haila, Juma'a, Biki, ko Wankan janaba). Sannan sai ki yi tsarki, ki wanke duk inda najasa ta taba, sai ki wanke hannayenki sau uku, sannan sai ki yi cikakkiyar alwala. Daga nan sai ki wanke kanki sau uku tare da cuccudawa, sai ki game jikinki da ruwa. Shikenan kin yi wanka.

Abin da dai yake muhimmi shi ne a game jiki da ruwa tare da cuccudawa.

_An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi wankan janaba, ya na farawa da wanke hannayensa, sannan ya zuba ruwa da damansa a bisa hagunsa, sai ya wanke farjinsa, sannan ya yi alwala, sannan ya kama ruwa, sai ya shigar da 'yan yatsunsa a cikin gashin kanshi, sai ya zuba ruwa a kanshi sau uku, sai ya wanke kafafunshi. Bukhary da Muslim suka ruwaito shi, lafazin Muslim ne._

Wannan shi ne sifar Wankan Manzon Allah (ﷺ)

 ~Wannan shi ne iya abin da na sani. Wallahu a'lamu.~

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*📞08166650256.*_

_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_
Post a Comment (0)