TAMBAYA
=========
👇
asslm mlm dan Allah aure zanyi kum gidan kishiya xani mlm dan Allah a temaka min d adduoin d xan dinga yi na Neman tsari daga kaidinta.
AMSA
=====
👇
Kina fadin HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL Allah zai tsareki daga kaidinta, da ma wadda ba ita ba.
Allah madaukakin sarki yace da Annabi Ibrahim ya furta kalmar HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL duk da bala'i irin na wuta wadda bala'inta da kiyayyarta ga Dan Adam tafi duk wani bala'in mutum haka tafi kiyayyar da kishiya take yiwa kishiyarta, lokacin da aka cewa manzon Allah saw wuta tayi Gobara a wani gida a garin madina, sai yace LALLE WUTA MAKIYARKU CE, IDAN ZAKUYI BARCI KUNA KASHE TA.
Lokacin da Annabi Ibrahim yace HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL sai wutar ta zama sanyi na aminci gareshi, harma Abdullahi Dan Abbas yace, in banda Allah yace ta zama sanyi na abinci, da sai sanyin da aka bata unarni ya cutar da Annabi Ibrahim.
Sabida haka duk kaidin mutum, wannan kalmar tafi karfinsa.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876