TAMBAYA TA 4

TAMBAYA ======= 👇 Assalamu alaikum warahmatullah, Amincin Allah yatabbata ga malam da ahalin gidansa, Daduk Wanda kecikin wannan zauren mai albarka, Dasauran alummar annabi baki daya, Allahumma Ameen. Su'aãl Malam ina hukuncin irin hakurin makka damu mata muke Saunawa idan munje saudiyyah? Shin idan mace tamutu za a iya binneta da wannan hakurin kokuma sai ancireshi? Shin minene matsayin Sawannan hakurin garemu? Ya halasta ko bai halasta ba? 🤔 AMSA ===== 👇 An taba min irin wannan tambayar wadda nayi ishara da cewar, Malamai sun danyi tsokaci akan rashin halaccin sanya wannan hakorin Sabida gudun riya karta shiga cikin ibadarki tsakaninki da mahaliccinki. Idan mukayi duba ga magabata da suka shuda a baya, zamuga yadda suke boye abinda yake tsakaninsu da Allah na ibada. Amma mu yanzu muna nuna abinda mukayi tsakaninmu da ubahlngiji. Wani daga cikin magabata, an bishi gidansa a lokacin da ya shigo masallaci yace ya Allah sai Kayi mana ruwa, Dan da nana kuma Allah ya saukar da ruwan, da wani ya bishi ya tambayeshi akan menene tsakaninnsa da Allah, da yake yiwa Allah har ya sami wannan matsayi? Da ya fahimci ana neman a gane tsakaninsa da Allah, nan da nan ya bar garin gabaki daya. Abuddar'da Allah ya kara masa yarda ya taba ganin wata mata da Dan sawun sallah a goshinta, Wannan Dan bakin da yake fitowa maslallata, sai yace da ita, dama wannan bai fito miki ba, Sabida yana guje mata kar riya ta shiga cikin ibadarta. Amma mu yanzu muna nuna ibadunmu ga Allah, idan munyi magana dashi an gani, idan muna kuka sai an gani, idan muna dariya sai an gani, anya kuwa ana karba mana? Alla ya shiryemu. Maganar idan kazo mutuwa kuma, za'a fidda miki ko ba za'a fidda miki ba, ban taba Jin wani magana akan hakan ba. Amma dai abinda ya dace, a fidda shi da zaifi. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)