GWAJE GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE A MATSAYAR SHARI'A

*_GWAJE GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE: INA MATSAYAR SHARI'AH?_* MUQADDIMA ▪Aure aya ce daga cikin ayoyin Allah, kuma ni'ima ce daga cikin ni'imominSa. *_“ومن آياته أن حلق لكم من أنفسكم أزواجا لتسكنوا إليها... {Ruum, 21} ولقد أرسلنا رسلا من قبلك وجعلنا لهم أزواجا وذرية { 38,Ra'ad}_* ▪Matukar an gina shi a bisa turbar kauna da soyayya da girmamawa da mutunta juna, aure na ba da kariya ga ko wa ne bangare na iyali; ya kyautata wa mutum tsarin rayuwa; ya haifar wa mutum da kamala; kuma yana ba da damar biyan bukatar sha'awa ta dabi'a. *_▪”وأنكحوا الأيامى منكم والصالحين من عبادكم وإمامكم“ {32 ,Nuur}_* *_▪”إذا تزوخ العبد فقد استكمل نصف دينه فليتق الله في النصف الباقي“ {Baihaki}_* *_▪”يا معشر الشباب من استطاع منكم الباءة فليتزوج“ { Bukhari; Muslim}_* ▪Wannan yasa Musulunci ya shar 'anta aure a matsayin halastacciyar hanyar hayayyafa da yawaita al'umma, tare da tabbatar da dorewar jinsin dan Adam; ya girmama al'amarin aure; ya karfafe shi; kuma ya hana dabi'ar kin yin aure. *_▪ ”فنكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع.. {4:3,Nissa}_* *_▪ ”تزوجوا الودود الولود، فإني مكاثر بكم {Abu Dawud; Nasaa'i}_* *_▪”تزوجوا فإني مكاثر بكم الأمم، ولا تكونوا كرهبانية النصارى {Baihaki}_* *_▪” يا عثمان، إن الرهبانية لم تكتب علينا، أما لك في أسوة حسنة! فوالله إني لأحشاكم لله، وأحفظكم لحدوده“ {Ibn Hibban}_* *_▪ ” النكاح من سنتي، فمن لم يعمل بسنتي فليس مني“ {Ibn Maajah}_* *_Hikimomin Aure_* ▪Yaduwa da dorewar jinsin dan Adam ▪Biyan bukatar sha'awa ta dabi'a ▪Samun natsuwa da sukuni da kwanciyar hankali ▪Karin matsayi a tsarin zamantakewa ▪Ma'aurata kan shiga cikin rayuwar aure da fatan samun walwala da jin dadi da farin ciki da soyayya da kauna mara iyaka. ▪Irin wannan guri kan samu tazgaro a lokacin da dayan ma'aura ya fahimci cewa abokiyar/abokin zama na tare da wata cuta ko larurar rashin lafiya da za ta yi karen tsaye ga cinma wadanda gurace-gurace. ▪Wannan ya sa a yau, masana harkokin lafiya ke ta nuna muhimmancin yin gwaje-gwajen lafiya ga maza da mata kafin su yi aure don a kauce wa hadurran da ke tattare da cututtukan da ke shafar ma'aurata a dalilin zaman tare ko suke iya shafar 'ya'yansu. In sha Allah za mu dakata anan sai kuma mun hadu a rubutu na gaba za mu ci gaba. *_Rubutawar: ✍🏼_* *_Sheikh Dr. Ahmad Bello Dogarawa._* Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)