MENENE HUKUNCIN SANYA NIQAB A MUSULUNCI?

*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,467:*
=
Menene hukuncin sanya nikab amusulunce, yadda hijab yake wajibi haka nikabi yake ko kuwa?
=
=
Amsa
=
_Toh wannan zance mafi inganci ba wajibi bane mace ta sanya niqabi matukar batayi shafe shafe a fuskar tataba. Duk da cewa anyi sa6ani akai tumtuni akwai wadanda suke ganin wajibine mace ta sanya nikabi kuma wannan shine ra'ayin mafi yawan malaman saudiyya. Amma zancenda yafi inganci a wajenmu shine ba dole bane mace ta sanya nikabi. Nasirudden Albani ya wallafa littafi guda uku akan wannan matsalar Nafarko sunanshi Hijabul Mar'a. Nabiyu Jalbabil Mar'a. Se na ukun kuma Arrddul Mufhim. To amma idan mace tashafa wani ado ko wata kwalliya ko hoda afuskarta wannan abinda yafi shine ta sanya nikabi, amma innatayi shafe shafeba to babu hujjar cewa dole tasa nikabi*****_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
19-08-1439
06-05-2018
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika
Post a Comment (0)