SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?

*_SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum Malam mai ciki za ta iya ganin Haila? *Amsa:* Wa'alaikm assalam Yawanci idan mace ta dau ciki jini yakan daina zuwa mata, Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan malamai sun yi sabani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a alqur'ani ko a sunna da zai hana shi ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i, kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun Ahmad. Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake tabbata ga mai haila mara ciki sai a gurare guda biyu. *1.* SAKI- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta idan tana haila, amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin haila, saboda sakin matar da bata da ciki ya sabawa fadin Allah (Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud Dalak aya ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. Amma sakin mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta, wannan ya hada da tana cikin haila ko tana cikin tsarki, saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan ciki, don haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima'i da ita. *2.* Mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba, saboda iddar ta tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan ya hada da tana haila ko bata yi, saboda fadin Allah madaukaki (Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne idan su ka haife cikinsu). Suratud Dalak aya ta 4 Don neman karin bayani duba: Dima'uddabi'iyya shafi na 11. Allah ne mafi sani 4/2/2012 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)