SHIN UWAR ADASHI ZATA IYA KARBAR LADAR ADASHI?

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,231:*
=
Nice uwar adashi idan na tara kudi sai akwasa to idan mutun ya kwasa wani yakan ban Yan kudi yace insai goro,amma kuma akwai wadanda basu bayarwa kuma duk Wanda ya bada bani ke cewa abaniba saidai ra'ayin mutum.To miye hukuncin kudin da nake amsa?
=
=
Amsa
=
_Toh gameda uwar adashi akwai bayani kamar haka: Na farko shine idan har ke badake akeyin adashinba kenan bakya ciki kawai daukoki sukayi sukasaki kiyi musu aikin tara kudadenda suka zuba duk idan sukai kwasa sesu baki wani kudi wanda aka kayyade to wannan babu laifi ya halasta. Idan kuma kema kina cikin adashen dake akeyi amma sekika zama kece kike tarawa to wannan kuma be halasta subaki komaiba a lokacin kwasa domin ke taimako kikayi dan haka sedai ayi fatan Allah yabiyaki idan kika kyautata ammasu bai halasta subaki komaiba. Amma kamar yadda kikace wasune suke baki ababin ihsani wasu basa bayarwa to wannan kuma akwai shubiha aciki wasu malaman suna ganin ya halasta kikar6a amma nidai bana tare dasu nafi natsuwada cewa karki kar6a idan mutum zeyi miki ihsanin to yabari daga baya in ankwana biyu seyazo yabaki ba a wannan lokacinba*****_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah a
nta astagfiruka wa atubu ilaika
Post a Comment (0)