MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKE MANA YANKAN RAGO;
2. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKE TARWATSAMU DA BAMA BAMAI;
3. MUNYI HAKURI LOKACIN DA SOJOJI KE MANA BINCINKEN KWA-KWAF GIDA GIDA;
4. MUNYI HAKURI LOKACIN AKE BINMU HAR MASALLATAI ANA KASHEMU;
5. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKA KARYA TATTALIN ARZIKIN AREWACIN NIGERIA,DA GAN-GAN;
6. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKA KARKASHE MANA MALAMAMMU DA MAHADDATA ALQUR'ANI;
7. MUNYI HAKURI LOKACIN DA GWAMNATIN TARAYYA TA HANA JIRAGEN YAN KASUWA SAUKA A KANO;
8. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKA KAIWA MANYAN MALAMAMMU HARIN KISA;
9. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKA KWASHE MANA QANNE DAGA MAKARANTAN KWANA, SU SAMA DA MUTUM DARI BIYU;
10. MUNYI HAKURI LOKACIN DA GWAMNATIN TARAYYA TA HANAMU SHIGA AIKIN SOJA;
11. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKETA KORAN 'YAN UWANMU DAGA AIKIN SOJA HAKA KURUM BA DALILI;
12. MUNYI HAKURI LOKACIN DA AKA HANA SOJOJINMU MAKAMAI DA ZASU YAKI BOKO HARAM, LOKACIN DA SOJA KE YARDA MAKAMINSA YA TSERE SABODA MUSIBA, DA BALA'I;
13. MUNYI HAKURI QARKASHIN MULKIN YANFASHI DA MUKAMI, GAGGAN MABARNATA, KUMA SHAHARARRUN BARAYI.
SABODA HAKA;
YAKAMATA MU HUCHI ZUCIYARMU, MU DAURE, MUYI HAKURI, LOKACIN DA SHUGABANMU KE KOKARIN KAWO GYARA KURA-KURAN DA AKA TAFKA NA TSAWON SHEKARU GOMA SHA SHIDDA, SHEKARA 16 BA KWANA GOMA SHA SHIDDA BANE. MU DAURE, MUYI HAKURI NA LOKACI KADAN DON GANIN AN SAITA KASARNAN BISA TURBA DAIDAITACCIYA.
IDAN KA SAMI WANNAN NASIHA, MUNA SOKAIMA KA TURAWA 'YAN GROUP DINKA DOMIN MU SAMU ALLAH YA HUCHIYARMU MUTANEN AREWA, YA BAMU HAQURIN JURE GYARAN DA AKESO AYI.
WANDA WANNAN GYARA KOWA ZAI AMFANA, MUSAMMAN MU MUTANEN AREWA.
MU DAURE, MU CIJE, MU DAINA TSINEWA DA MUGWAYEN ADDU'O'I GA GWANNATIN
BUHARI.
Tags:
Siyasa (politics)