BAMBANCI {24}
HABBATUS SAUDAH
Bayan Nassi ya tabbatar da cewa: Tana maganin cututtuka da dama, amma ba a bayyana mana ga yadda ake hadata wajan yin maganin kaza da kaza ba, wannan wani irin ilimi ne daga cikin ilimin Allah da yake baiwa waɗanda yaga dama ta hanyar tunani ko ilhama ta yadda za ayi nazari sai a auna ko a gwada cewa: idan an hada kaza da Habbatus saudah yana tasiri wajan matsala kaza, kowa da yadda Allah ya fahimtar da shi yadda ake amfani da Habbatus saudah wajan magance cututtuka mayawaita ciki har da waɗanda magungunan turawa suka gaza samar da shi.
Habbatus saudah ba ta buƙatar wani dogon bayani a kanta saboda kusan duk ansan ta ta shahara sai dai ayi karin bayani akan wasu daga cikin amfaninta ba ma iya cutar jinnu ko sihiri ba, Habbatus Saudah tana shiga cikin magungunan wasu cututtukan zamani waɗanda suka shafi gudanar jini kamar su hawan jini, cutar diabetes (sugar) da sauran su, ga kadan daga cikin amfanin da take yi da yadda ake hada su:
1- Ana karanta wasu Ayoyin Alqur'ani ( duk Aya ko surar da kaso karantawa ( idan da hali a karanta Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Ikhlas, Falaqi da Nasi) a cikin Man habbatus saudah da jan miski, sai a rika shafawa a jiki da kuma kai ko tsakiyar kai da kuma tafin kafa da tsakanin yan yatsu kullum da daddare, domin hakan yana matuƙar takurawa duk wani jinnun da ke a jikin mutum kuma har Allah yasa shi jinnun yaji an takura masa sai ya fice abinsa da izinin ALLAH.
2- Mai fama da matsalar hawan jini ko cutar diabetes (Sugar) zai rika shan man Habbatus saudah cokali 1 kullum da safe daga da yayi karin kumallo, saboda yana daidaita jini kuma yana tace sugar da take a cikin jini, Insha ALLAHu.
3- Ana yin hayaqi ko turare da ya'yan ta, ta yadda hakan yakan takurawa Shedanun da ke a jikin mutum da ma waɗanda ke a cikin dakin ko gidan saboda ba sa son warinta, kuma idan anyi turaren hayakin a cikin daki yana korar qwarin da ke cikin daki kamar: Kyankyaso, sauro, da duk wani nau'i na kwarin da ke zama ko shiga dakunan mutane.
4- Man Habbatus saudah yana matukar amfani wajan karawa gashi.da fata lafiya kuma idan aka rika sanya shi a kai laziman yana hana kawo furfurar wuri kuma yasanya gashi ko gemu yarika kyalli da walkiya, insha ALLAHu.
5- Ana iya amfani da ita a fannoni da dama wa'danda Allah ne kaɗai yasan adadin su dai dai kowa yayi iya yadda zai iya. *Shawara dai anan shi ne: Duk wani magani kamata yayi ka rika sanya masa habbatus saudah a ciki, a abincinka ma ka rika sanya man Habbah, a mayukan shafawarka ma haka/ki ma haka, Insha ALLAHu za ka dace da izinin ALLAH.*
Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji Amfanin *garafuni* wajan magance matsalolin mayu da shafar Jinnu da sihiri.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)
Gmail:
rismawy86@gmail.com
WhatsApp :
+2348031542026
Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine