DUK LOKACIN DA...

Duk lokacin danazo kwanciya na kashe fitilar dakina,dakina yayi duhu,,, a lokacin babu abinda nake tunawa sai lokacin da za'aje a sakani a kabari gurin da babu fitila balle na tashi nace zan kashe, Gurin da babu fadi balle nace zanyi juye-juye idan ina kwance Gurin da bazan taba sanin lokacin damina ne yanzu ko lokacin zafine ko kuma lokacin sanyi ne ba, Duk lokacin dana tuna wannan lokacin zuciyata tanayin firgici sosai, Lokacin da za'aje a binne ni a dawo a barni a cikin wannan duhun Cikin wannan zafin dan babu fanka babu A.C Sai abunda na shuka a nan duniya sai halina shine abokin zama, Shine:- fanka ta Haskena A.C na Ya Allah kasa aikin mu kar6e66e ne a gurin ka Ya Allah kasa ranar mutuwar mu itace ranar hutun mu,arzikin mu, Ya Allah kasa muna cikin masoyan ka Ya Allah ka azurta mu da mutuwar shahada Ameen ya rabbi

Post a Comment (0)