Gyara Kayan Ka

Gyara Kayanka Dan uwa🤝 Abin kunya ka yi saukar digiri ta farko, wani ma ta biyu, wani kuwa ya yi ta uku (PhD), amma baka sauke Alkur'ani ba. Duk littafin da aka rubuta da turanci zaka iya karantawa amma ba ko'ina zaka iya karantawa na Alkur'ani ba, kuma ba kwakwalwace baka da ita ba, kawai sakaci ne ,da kuma rashin damuwa da addinin. Idan mutum ya tsinci kansa a cikin masu wannan sifa ,to, ya yi kokari ya gyara, domin lokaci bai kure masa ba, sai dai ya tuna rayuwarsa qarewa take qabari yana dada kusantarsa, idan mutum yaje qabari baza'a tambayeka komai game da karatun boko dinkaba (qualification),ko kuma daular da ka tarawa 'ya'yanka, ka Sani duk san da kaga ana nunama kana raye ne kawai kuma kana da dukiya,da zarar ka mutu wasu wallahi sun manta da kai har iyalanka wasu damuwa zasuyi araba gado domin suyi fa caka da dukiya,kai kuma kana qabari daga kai sai Aikin daka aikata, babu air condition ballantana gado, ko kasan ya qabarinka yake a ynxu? Ko sau dayane ka dinga tunawa kanka kwanciyar qabari ko karage buri a rayuwarka, kabawa kanka da duk Wanda yakamata tarbiyya ta addini da abincin ruhi wato AL-KUR'ANI, ka gina tarbiyyar 'ya'yanka,ka nuna musu ba wai Kaine gatansuba wannan tarbiyyar ta addini da ilimin QUR'ANI shine gatansu duniya da lahira, ko bayan ranka zasuyi maka addu'a kuma zata iskeka... Allah ubangiji ya sa mun dace ameeeen summa ameen. Abubakar musa ( caleepha)

Post a Comment (0)