✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
ABOKIN FIRA
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto
*KARSHEN MAROWACI*
Wani Alhaji ne aka yi dan birni mai yawan arziki. Yana da dukiya sosai da shaguna masu yawa a kasuwa, amma kuma marowaci ne na
kin karawa. Watarana ya sawo kaji guda biyu ya kawo ma matarsa don ta gyara su yi kalaci. Suna cikin cin naman kajin nan suna fira sai wani
bawan Allah ya kwankwasa kofa. Sai Alhaji ya ce ma matarsa, tashi ki bude kofa ki gani ko wane ne. Da ta dawo sai ta ce, wani bawan Allah
ne da yake neman abin da ya ci. Nan take sai ya hau ta da fada yana cewa, su irin wadannan mutanen ba su bari sam mutum ya samu
natsuwa a cikin iyalansa. Ta yi ta lallashin sa don ya amince ko dan hince ta ba wannan bawan Allan daga cikin naman kajin nan amma ya ki. Daga karshe dai ya tashi da kansa ya ingiza masa kofa kamar zai
ture shi.
A kwana a tashi sai aka yi gobara a kasuwa. Gobara kuwa sai ta lashe duk shagunan Alhaji ba ta rage masa ko guda daya ba. Da ya dawo ya sanar da matarsa sai ta yi ta ba shi haquri tana neman ya mayar da al’amari ga Allah, Allah zai saka masa, amma Alhaji ko ta bayan kunnuwansa wannan wa’azi bai bi ba. Ya shiga damuwa matuka kuma ya rasa wanda zai taimaka masa don ya dawo da jarinsa. Duk wanda ya je wurin sa sai ya kore shi yana tuna masa wata nasiha da ya nema a wurin sa bai samu ba. Nan take sai talauci ya kwankwasa masa kofa. A kwana a tashi ya kasa rike matarsa saboda babu abin
ciyar da ita, sai ya yanke shawara ya ba ta takardar saki ya ce ta koma gidan iyayenta. Bayan da ta yi idda ta kammala sai Allah ya kawo wani Attajiri mawadaci ya aure ta.
Watarana, suna zaune tare da maigidanta suna cin naman kaza sai wani bawan Allah ya kwankwasa kofa yana cewa, ku ba ni na Allah, Allah ya ba ku mu samu. Sai mijin nan nata ya ce, tashi ki dauki kazar nan daya ki kai ma wannan mabukaci, mu dayar ma ai ta ishe mu. Da ta dawo sai mijin ya gan ta tana ta kuka. Ya tambaye ta, me ya faru?
Sai ta ce masa ai mijinta ne na farko. Shi kuma sai ya kada baki ya ce mata, ni kuma ai ni ne almajirin nan da ya kora.
*Darussa:*
👉 Duniya rawar ‘yan mata ce. Idan ta juya na gaba ne yake komawa baya.
👉 Idan Allah ya ba ka ka taimaka ma wanda bai ba shi ba.
👉 Babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai Allah.
👉 Alheri gadon bacci ne, mugunta kuwa Karya ce, mai ita takanbiya.
⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08036487324, 08038977817, 08034453678, 08036958490