HUKUNCIN KARIN GASHI A SHARI'A

*_Tambaya ta (415)_*
:
_Shin a *Shari'ance* Menene hukunci gameda karin gashi da Mata sukeyi a Kansu??_
:
*_Amsa_*
:
_Dukkan *Mālamai sunyi Ittifāƙi* akan cewa bāya halatta ga dukkan wata Mace tayi amfāni da gāshin wani *Ɗan-Ādam* Mace ko Namiji don tayi *Ƙārin-Gāshi* dashi akanta, wannan kam harāmunne *Ƙaulan-Wāhidan,* Mālamai sunkafa *Hujjarsune* da Hadisan *Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* da sukazo akan haka, daga cikinsu akwai wannan Hadisi da *Aηηαвι(ﷺ)* Yake cewa:_
:
*"لَعَنَ اللَّهُ الْوَاصِلَةَ وَالْمُسْتَوْصِلَةَ......إلخ"*
*_MA'ANA:_*
*_Aʟʟαн(ﷻ) Yā tsīnewa Mātar datake (sana'ar) Ƙārin-Gāshi, dakuma Mātar da'akeyiwa Ƙārin-Gāshin......,_*
:
_Danhaka harāmunne bai halattaba, to amma Saidai *Mālamai sunyi Saɓāni* akan cewa Shin wannan haramci yashafi dukkan kowanne irin nau'in *Gāshi* ko wani abu da Mace zata iya amfani dashi tayi *Ƙārin-Gāshi* akanta, kokuma ā'a haramcin yā *taƙaitane kaɗai* akan yin amfani da asalin *Gāshi-Mutum?* wani *Sāshe* na Mazhabobin *Hanafiyya* da *Hanābila* suntafi akan cewa indai ba *Gāshin-Mutum* bane to yā halatta Mace tayi amfani dashi, wāto kamar irin su *Zaren-Ūlu, Zaren-Roba, Ƙyallen-Yādi, Gāshin-Dabbōbi,* dadai sauran makamantansu, amma Mazhabin *Mālikiyya* tāre da mafi yawa daga cikin *Mālamai* sun ɗauki *(Umūm)* na wannan Hadisine, danhaka sukace wannan haramci yashāfi kowanne irin nau'i na *Gāshi,* ko wani abu dabam wanda za'ahada dashi ayiwa Mace kitso a kanta, sukace haramunne bai halattaba ayi, dalilinsu kuwa shine, baya ga *(Umūm)* na wancan Hadisi, sukace akwai wani Hadisin da *Al-Imāmu-Muslim* ya ruwaito wanda  Yake cewa:_
:
*"زَجَرَ النَّبِيُّ (ﷺ) أَنْ تَصِل الْمَرْأَة بِرَأْسِهَا شَيْئًا"*
*_MA'ANA:_*
*_Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) Yā tsāwatar gameda cewa kada wata Mace ta haɗa Gāshinta da kowane irin abu,_*
:
_Sukace wannan Hadisi yā game *Kōmai-da-Kōmai* bawai sai *Gāshin-Mutum* kaɗaiba, sukace kōma menene bai halattaba, kamar Mace take amfani da *Gāshi* irin na *Company* da'ake sayarwa a *Kanti,* hakanan wasu daga cikin *Mālamai* sukace haramunne Mace tayi amfani da dukkan wani abu wanda zaisa kanta yayi tudu aga kamar cewa ai tana da *Gāshine* dayawa akanta, alhāli kuma ba yawan *Gāshi* bane, kawai *tāyi cōge ne da algus,* hakanan harāmunne *Mace-Musulmā* tasa *Hūlar-Gāshi* akanta, wacce ake ƙiranta da *Lārabci (الباروكة)* domin kuwa itama hukuncinta yashiga cikin wancan Hadisi, koda yake akwai *Mālaman* da suke ganin ya halatta ayi amfani da'ita, amma magana mafi inganci haramunne, Sannan kuma sanyata yazama anyi kamanceceniya da *Mātan-Kāfirai,* wanda wannan ma kaɗai yā isa yazama *Hujja* na haramcin yin amfāni da'ita, to amma idan yakasance Mace tasamu wata larurar da tasa gaba ɗaya *Gāshin-Kanta* yazube, kanta yazama ba *Gāshi* kamar anyi mata aski *Ƙwal-Ƙwal,* kokuma Mātar datake da *Sanƙo* akanta gaba ɗaya ba *Gāshi,* anan sai wasu daga cikin *Mālamai* sukace ya halatta tayi amfani da *Hūlar-Gāshi* dan tarufe aibun dake tare da'ita, domin batayi hakan da nufin ado ba dan taƙāra kyau, saidai tayine dan tarufe larurar dake kantane kawai, to amma Saidai mafi yawan *Mālamai* suntafine akan cewa koda kanta *Ƙwal-Ƙwal* yake bābu *Gāshi* to duk dahaka bai halattaba tayi amfani da *Hūlar-Gāshi,*_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαn*
              *08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"كفاية الطالب الرباني" (2/459)*
:
*"فتاوى اللجنة الدائمة" (5/191)*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)