KALLON QUR'AN A SALLAR TUHAJJUD

_*Tambaya:*_

Assalamualaikum, Dan Allah malam menene hukuncin kalon Qur'ani  a sallar tahajjud

_*Amsa:*_

_Ya halatta mutum ya dauki Alqur'ani a sallar Tahajjud idan yana da karancin hadda, kuma yana so ya tsawaita karatun._

_Kuma ya halatta ga mai bin liman shima ya bude Alqur'ani domin bin liman ko koya. Kuma ta hakan za su iya gane idan liman ya yi kuskure su yi mai gyara, ko in ya kakare su tada shi. In shaa Allah._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Post a Comment (0)