YAƘIN BADAR



YAKIN BADAR (17- RAMADAN)

Via:- Garkuwan Magabata

Kamar irin wannan rana ce ta sha bakwai (17) ga watan ramadan Allah(s.w) ya yiwa shuwagabanninmu,gishirin addinin musulunci, garkuwan musulunci, zaratan sahabban muhammadu rasulullah(s.a.w) baiwar gwabzawa a yakin badar.

Allah ya karrama, ya fifita sahabban da nayi yakin badar fiye da sauran sahabbai radiyallahu anhum. Kamar yanda wannan hadisin ke fada mana.
ﻭﺭﻭﻱ ﺃﺑﻮ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ " ﺍﻃﻠﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﺪﺭ ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﺃﻫﻞ ﺑﺪﺭ ﺍﻋﻤﻠﻮﺍ ﻣﺎ ﺷﺄﺗﻢ ﻓﻘﺪ ﻏﻔﺮﺕ ﻟﻜﻢ "
Allah yana cewa" duk wanda ya halarci yakin badar ya aikata abinda yake so an gafarta masa. ma'ana an basu abinda ake cewa"Freedom in life" ba'a kama su da laifi. 

Amma ba haka kawai bane Sahabbai suka samu wannan romon ba. Bari muji kadan daga cikin fafutukar da 
Sahabbai (r.a)suka yi. Sun halarci yakin badar suna su 313 domin ba kowa yasan za'a tafi wannan yaki ba, sahabbai sun fita cikin tsananin zafin rana suna dauke da azumi, ranar jumu'a 17 ga watan ramadan kuma mafi yawan sahabbai kasa suke tafi basu da takalmi, sahabbai sun je yakin suna da doki biyu (2), sulke guda shidda (6) da takubba guda takwas (8). 

Ku duba fa! Mutum 313 amma da takobi takwas ko dame sauran zasu yi fada? La haula wala quwata illa billah! Sahabban nan 313 akwai muhajirun da lansaru a cikinsu, muhajiruna suna da sahabi 77 wanda a dauke da tutar muhajirun shine Aliyu ibn abu dalib(r.a)Lansaru suna da sahabbai 236 wanda a dauke da tutar lansaru shine sa'adu ibn ubada (r.a). Kafin a fara yakin badar an kamo wani mutum(kafiri) sai Annabi(s.a.w) ya tambe shi su nawa suke ? Sai yace suna da yawa, sai Annabi (s.a.w) yace masa me kuke ci kullum? Sai yace rakumi tara ko goma ake yanke masu kullum, sai Annabi(s.a.w) yace kenan hakan ya nuna su dari tara (900) suke zuwa su dubu (1000) ko wane mutum dari suna canye rakumi guda. Wannan ya nuna girma,basira da fahimta irin ta manzon Allah (s.a.w).

Daga nan sai aka je filin gwabzawa dama Allah(s.w) yana cewa
کم من فیٸة قلیلة غعلبت فیٸة کثیرة بإذن الله
....."ma'ana jama'a yar kadan tana galaba akan jama'a masu yawa" da haka ne Allah ya taimake sahabbai su 313 suka yi nasara akan kafirai mutum 1000.

A gefen musulmi an kashe mutum goma sha hudu (14) takwas (8) cikin lansaru, shidda (6) cikin muhajirun. A gefen kafirai kuma an kashe saba'in (70) an kama saba'in (70) daga cikin wadanda aka kashe akwai Abu jahil, wanda wasu yara da ake kira MU'AZ da MU'AWIZ diyan Af-ra'a ne suka kashe shi. 

Wato abinda ke faruwa wadan nan yaran mu'az da mu'awiz sun je wajen wani dattijo suka tambaye shi cewa" yasan Abu jahil? "Yace masu eh! Sai suka ce suna son idan aka fito fili ya nuna masu shi. Ana fitowa kafin a fara gwabzawa sai tsohon nan ya kira yaran su biyu ,suka zo sai yace masu kun ga mutumin can na saman doki mai kwalliyar zinare? Suka eh! Yace shine a Abu jahil.wallahi nan take yaran nan suka ruga a tare rike da mashi suka sokawa Abu jahil ya fado daga saman doki a mace.

Daga wannan yaki na badar Allah (s.w) ya karya logon kafirci daga nan kuma tutar musulunci take kadawa har zuwa yau. Bayan kammala yaki sai aka zuba su Abu jahil cikin wata rijiya.sai Annabi(s.a.w) yazo yana kirari a bakin rijiyar yana cewa su Abu Jahil"Ina alkawalin da ubangijinku ya yi maku? Ga shi namu ubangiji(Allah) ya cika mana nashi alkawali"sai sahabbai suka ce ya manzon Allah sun mutu ai basu jinka,sai yace" a'a ku da anan baku fisu jin abinda nake fada ba. A wajen yakin duk inda Annabi yayi yana tare da sayidina Abubakar(R.A) a gefensa na dama sai sayidina umar a gefensa na hagu. 

*Allah ka sakawa wadan nan sahabbai da Alheri gaba dayansu Ameeen.*👏🏾👏🏾

  ✍🏿Nafi'u haruna bello
Post a Comment (0)