KYAKKYAWAN NAZARI

*KYAKYKYAWAN NAZARI*
*_MAI ARZIKI_*; Shine Wanda Talaucinsa bai hana ya taimaki dan uwansa da- abinda yake da shi ba, koda kuwa shi kadai yake da shi.
*_TALAKKA_*; Shine wanda yana da halin taimakon sama da mutum ashirin, amma ba wanda za'a nuna ace ta hanyarsa ya samu arziki ba.
*_WANDA YAYI ASARA_*; Shine Wanda Allah bai bashi arziki ba Amma kuma kullum yana gidaje, office, da kuma majalissun mutane yana Rokonsu.
*_MAI RABO DUNIYA DA LAHIRA_*; Shine wanda Allah Ya daukaka darajarsa ya bashi dukiya Amma kullum gurinsa yaga ya taimaki wanda baida.
*_MARAR RABO_*; Shine wanda Allah ya bashi wata baiwa amma kuma alfahari kullum a bakin sa yake.
*_MATACCE_*; Shine wanda kullum baya tunanin aikin da zaiyi ya samu lada.
*_RAYAYYE_*; Shine wanda idan ya mutu lada zata riqa samunsa a Qabarinsa.
_1. Idan naira ashirin kake da ita, idan kaga wani na neman 15 bashi ka rike naira 5 ka zama mai arziki, dan wani ya ci ta kasan ka._
_2. Idan Allah ya hore ma arziki, ko masana'anta yi kokari ka gina wani shima ya zamo kamarka, kafita daga jerin talakkawa._
_3. Idan bakada kuddi ka dogara ga Allah harya baka kada kaje gidan wani nema, kada ka kai karar Allah wajen wani Mutu, Allah ne ke bayarwa kuma shi ke hanawa._
_4. Idan Allah ya baka Dukiya kuma kana taimako kara taimakawa dukiyarka ta qaru anan duniya kuma a lahira ka samu lada._
_5. Idan Allah ya baka BAIWA ka gode masa kuma ka roqi Allah ya tsareka da aikata alfahari, zaka samu rabo duniya da lahira._
_6. Idan safiya ta waye kayi tunanin me zakayi wanda zai amfani Al'umma._
_7. Idan safiya ta waye kayi tunanin yin wani aikin Alkheri wanda ko bayan ka mutu zaiyi ta watsuwa a bayan kasa irinsu, GINA MASALLATAI, RIJIYA, DASA ICCE, BIYAWA TALAKKA WANDA ZAIYI AURE SADAKI, SADAKAR ALQU'ANI, SAKA 'YA'YAN TALAKAWA MAAKARANTA dss._
Haka kuma Idan ka tura Wannan Rubutun ga abokin ka Shima *SADAQATUL-JARIA* ce
YA Allah kasa mu dace kasa mu mutu da imani, kuma mu cika da kalma madaukakiya.
# ADMIN
Mukhtar Ahmad Muhammad
DA'AWAH COMMITTEE OF SUNNAH

Post a Comment (0)