*_Tambaya ta (291)_*
:
_Malam Menene Hukuncin *auren Kashe-Wuta* a Shari'ance??_
:
*_AMSA_*
:
_Wato dai Abinda ake ƙira da suna *Auren-Kashe-Wuta* shine, *Mutum* yasaki *Matarsa* har Saki(3), kuma daga baya sai yaji yanason yadawo da'ita to kuma babu damar yinhakan a *Shari'ance*, to shine sai *Mijin* suhaɗa baki da wani abokinsa akan cewa abokin ya aureta daga baya kuma yasake sai takoma gidan tsohon *Mijinta*, wato dai anufinsu shine kamar sunyiwa *Shari'ar Aℓℓαн(ﷻ)* wayo kenan, *Ko-Shakka-Babu* cewa *auren Kashe-Wuta* haramunne bai halattaba, kamar yadda yazo acikin *Hadisi Mαɳzσɳ Aʅʅαԋ(ﷺ)* Yana cewa:_
:
*"لعن الله المحلل والمحلل له" (رواه أبو داود)*
*MA'ANA:*
*_Aℓℓαн(ﷻ) Ya tsirewa Mai Halattawa (mai Auren Kashe-Wuta) dakuma wanda za'a Halattawa (tsohon mijin kenan)_*
:
_Danhaka kenan idan *Mutum* yasaki *Matarsa har Saki(3)* to bai Halatta yadawo da'itaba dole sai ta auri wani *Mijin* kuma *ingantaccen aure,* kuma bawai ya aureta bane da nufin nangaba yasaketa dan takoma wajen *tsohon Mijintaba,* Sannan kuma *Sharaɗine* yakasance Mijinda ta auraɗin *yataɓa Jima'i da'ita aƙalla koda sauɗayane*, to idan *Mijin yarasu* kokuma yasaketa dan raɗin kansa, to ya halatta takoma wajen *tsohon Mijhnta* ya aureta, amma idan yazamana cewa Sabon *Mijin* da taura *baitaɓayin Jima'i da'itaba* harsuka rabu dashi, to haryanzu batazama halal ga *tsohon Mijintaba* dole sai tasake wani auren kenan,_
:
_Amma idan yakasance *Mijin* dayasaki *Matar* saki uku, dama *sunhaɗa bakine* dashi da wani abokinsa dakuma ita *Matar* akancewa shi abokinnasa ya Aureta inyaso daga baya sai yasaketa tadawo wajen *tsohon Mijinta,* to ko shakka babu cewa wannan haramunne kuma *Kaba'irace daga manyan zunubai,* Sannan kuma shi wanda *ya auretaɗin* danufin haka *aurensu da'itaɗin Ɓataccene a Shari'a,* idanma yasadu da'ita to *Zina kawai sukayi,* hakanan kuma koda ya saketa to bai halattaba takoma wajen *Mijinta nafarkonba,* idankuma hartakoma yasake aurenta to sutabbata cewa *zaman Daduro (zina) sukeyi,*_
:
_Amma idan shi wanda ya auretaɗin babu wani haɗin baki dasukayi da *tsohon Mijinnata* wataƙilama shi *tsohon Mijinnata* baisanma cewa wannanɗin zai *auretaba,* amma shikuma wanda zai *auretaɗin* dama azuciyarsa yanaso kawai ya aureta dan yasaketa taƙara komawa wajen *tsohon Mijinta*, to shima aurensa da *Matar Ɓataccen aurene* sakamakon mummunar niyyarsa kuma shima in yasadu da'ita to zina kawai sukayi, danhaka shima koda yasaketa to baihalatta takoma wajen *Mijinta nafarkoba,*_
:
_Amma idan yakasance ita *Matar* dama azuciyarta tanasone ta auri wani danufin cewa idan suntare daga baya zatanemi yasaketa kokuma tayi ta munana masa haryagaji yasaketa, to anan sai *Malamai sukayi Saɓani,* Mazhabin *HANABILA* dakuma wasu daga cikin *Malamai* kamar irin su:_
*_Hasanul-Basriy,_*
*_Ibrahimun-Nakh'iy,_*
*_Shaikhul-Islam Ibn-Taimiyya,_*
_Sukace shima wannan nau'ne na *auren Kashe-Wuta,* danhaka shima bai halattaba sakamakon mummunar niyyarta, *Sannan sukace idan ɗaya daga cikin su ukun (wato mijin ko matar kokuma shi wanda zai aura)* yayi nufin ayi auren kuma daga baya asaketa takoma wajen nafarko, sukace duk hukuncinsu ɗayane auren baiyiba,_
:
_Saidai *Mazhabin MALIKIYYA* dakuma wani sashe na *HANABILA* sukace idan har yasaketa to ya halatta takoma wajen *tsohon Mijinta* sukace niyyarta na *auren Kashe-Wuta* batada wani tasirin da zata ɓata aurensu, Saidai wasu daga cikin *Ma'abota Ilimi* sukace *Maganar farko tafi ƙarfi,* tunda asali bai halatta takomaba harsai tayi ingantaccen aure, amma yanzu taje tayine da nufin nangaba takashe auren awani lokaci sananne sukace bai halattaba, domin yazama kamar tayi auren *Mut'ane kenan*, Sannan kuma gashi ta yaudari Mijin, ta cutar dashi, ta munana masa, dankawai yasaketa,_
:
_Saidai Mafi yawa daga cikin *Malamai* sukace idan har *Mijinta* nabiyun yasaketa to yahalatta takoma wajen *Mijinta* nafarko, sukace duk wanda igiyar aure ba ahannunsa takeba to niyyarsa ta rabuwa batada wani tasiri, domin *bata da'ikon ta'iya sakin kanta dakanta dole sai ansaketa,* Saidai abinda tayiwa *Mijin* na yaudara da munanawa sukace ananne takeda laifi, da kamata yayi ace tayi amfani da hanya maikyau wacce Mijin bazai cutu sosaiba, wato ta lallabashi har ya yarda suyi *Khul'i* ta mayar masa da *Sadaƙinsa*, hakan shiyafi dacewa:_
*(وَالـلَّـهُ سُـبْـحَـانَـهُ=وَتـَعَــالـَيٰ أَعْـلَـمُ)*
:
*_Doмυn nЄMan Ƙarin bayani sai aduba waɗannan Լitattafai kaMar Ӈaka:_*
*_↓↓↓_*
:
*"شرح مسلم" (3/10)*
:
*"الفتاوي الكبري" (6/298)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (7/138)*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
🇷 🇺🇧🇺🇹🇦 🇼🇦
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
*_Domin sђiﻮa sђaŦinmu daкє Ŧaςєbooк sai asђiﻮa wannan linк кawai aאi ""liкє""👇🏾_*
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi