MACEN DA TAYI SANADIYYAR MUTUWAR 'YAR TA BISA KUSKURE ZATA YI KAFFARA?

*_Tambaya ta (272)_*
:
_*Mace* ce ta tafasa ruwan zafi amma batare da tasaniba sai *'Yarta ta rarrafo* tajanyo wannan ruwan zafin akanta wanda hakan yayi sanadiyyar *mutuwarta,* to ita Uwar zatayi *kaffarane* kokuma a'a??_
:
🇦 🇲 🇸 🇦:
:
_*Alal-Haƙiƙa* Wannan wani hukuncine da za'a'iya ginashi akan *Sakaci* ko rashin *Sakaci* *taɓangaren ita Uwar Yarinyar*, Misali: idan yakasance abisa al'ada wajen dasukeyin *Girke-girkensu* na yau da kullum dama wajene da yake kusa da inda *Mutanen gidan suke zaune,* to kuma bayan ta tafasa ruwa acikin *ɗakin girkin* sai tafita waje amma batare da tasaniba *'Yarta ta rarrafo* tajanyo wannan ruwan zafi akanta yayi sanadiyyar mutuwarta, wasu daga cikin *Malamai* sukace bazatayi *kaffaraba,* domun azahiridai babu wani *Sakaci datayi akan wannan 'Yartata*,_
:
_Amma inda ace ita *Uwar* dama tare suke da *'Yartata* awajen datakeyi *girkin* amma sai tafita waje tabar *Yartata agurin,* kokuma dama taga *'Yartata* tana wasa akusa dawajen amma *taƙi taɗauketa* tacanjamata waje, kokuma tariga ta sauke wannan *ruwan zafi* daga kan *murhu* ta ajjeshi *aƙasa* amma batareda tarufeba ko tasashi awajen da tasan cewa da wahala *ƙaramin yaro ya'iya ƙetarewa yashiga,* kokuma ta ajjeshi awajen da abisa al'adar gidan dama yara sukan iya shiga wannan wajen, to a'irin wannan yanayi idan *'Yartata tafaɗa cikin wutar kokuma tajanyo tukunyar girkin* tazubo akanta wanda hakan yayi sababin mutuwar ita *'Yartata*, to ko shakka babu akwai *Sakaci* dakuma *ganganci taɓangaren ita Uwar*, danhaka wajibine akanta tayi *kaffara* domun tayi kisan kaine abisa kuskure, *Alal-Haƙiƙa Malamai Ahlul-Ilmi* sunyi Maganganu sosai dangane da hukuncin *Matar* da *Ɗanta yamutu adalilin Sakacinta,*_
:
_Kamar Misalin *Matar* da take kwance tare *Ɗanta* akusa da'ita, amma batasaniba cikin barci tayi juyi *ta danne ɗan har yamutu,* kokuma ta *lulluɓe yaron gaba ɗaya da mayafi* batare da tafitar masa da kansa awajeba yadda *zai iya samun damar shan iska,* wanda kuma hakan yayi sababin *mutuwar yaron* saboda babu *iskar da zai iya shaƙa*, kokuma tazo tazauna akan yaron abisa rashin sani ko mantuwar cewa yana kwance awajen, *wanda hakan yayi sababin Mutuwarsa,* ko kuma zata bawa yaron wani magani amma *sai tayi kuskure taɗauko kwalbar datake ɗauke da guba (poison)* aciki tabashi yasha yamutu, kokuma *Mutum yayi Sakacin ajiyar*_
_*Maganin Ɓera (Rat poison)* akusa da inda yara zasu iyagani suɗauka, kuma yaro *yaɗauka yasha yamutu*, dadai sauran dukkan wani *kisan kuskure mai kama da wannan,* to wajibine akan *Mutum yayi Kaffara* tahanyar yin *azumin wata biyu ajere*, to amma inda ace babu wani sakaci da'akasamu *taɓangaren Mutum,* wato yayi iyakar *ƙoƙarinsa* wajen kiyaye dukkan wasu *Sharuɗɗa* dayasan zasu iya haddasa faruwar hakan, sannan kuma *yariƙi dukkan wani Sababi* don kaucewa faruwar hakan, Saidai kawai dama *Aℓℓαн(ﷻ) Yariga Yaƙaddara* cewa sai haka tafaru, to ayanayi irin wannan Mutum bazaiyi wata *Kaffaraba saboda babu wani Sakaci ko ganganci dayafaru ta ɓangaresa*,_
*(وَالـلَّـهُ سُـبْـحَـانَـهُ=وَتـَعَــالـَيٰ أَعْـلَـمُ)*
:
*_∂σмυи ηємαη кαяιη вαуαηι ѕαι уα∂υвα ωα∂αηηαη ℓιтαттαƒαι кαмαя нαкα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"المحلي بالآثار" (11/15)*
:
*"فتاوي اللجنة الدائمة" (21/366)*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
             *_Dαgα Zαυяєи_*
          *_Fιƙ-Hυℓ- Iвα∂αт_*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
    🇷 🇺🇧🇺🇹🇦 🇼🇦
         *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
             *_08032531505_*
*_┈┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈┈_*
_domin sђiﻮa sђaŦinmu daкє Ŧaςєbooк sai asђiﻮa wannan linк кawai aאi ""liкє""👇🏾_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)