WAI MAKIRCIN MATA YAFI NA SHEDAN Sau Dayawa zaka gan wasu suna yawan karanta wannan Ayar ko ma su kawo Ayar a Facebook kamar yadda nagani yanzu domin su nuna girman makircin Mata, wani lokaci har ma kaji suna cewa shedan ma yana tsoron kaidin Mata, sai kaji suna cewa ai Allah ma ya fada:- ﺇﻥ ﻛﻴﺪﻛﻦ ﻋﻈﻴﻢ * Lalle kaidinku yana da girma. Da farko dai ba Allah Madaukaki bane ya fadi hakan kai tsaye, shi Allah ya ambata mana abinda Azizu Misra ya fada ne, don haka maganar Azizu Misra ba zai zama hujja ba. Sannan ai ita Matar Azizu Misra ba wani abu ta kullawa Annabi Yusuf (Alaihissalam) ba face ta nuna masa so kuma ta bukaci suyi soyayya, wannan fa shine kaidin nata! Amma mu Maza bari kuji kaidinmu wanda yafi na Mata girma, lokacin da Annabi Yusuf ya gayawa MahaifinSa irin mafarkin da yayi sai Mahaifin nasa yace masa:- ﻳﺎ ﺑﻨﻰ ﻻ ﺗﻘﺼﺺ ﺭﺅﻳﺎﻙ ﻋﻠﻰ ﺇﺧﻮﺗﻚ ﻓﻴﻜﻴﺪﻭﭐ ﻟﻚ ﻛﻴﺪﺍ * Kada ka gayawa 'yan uwanka mafarkin da kayi har su kulla maka wani irin kaidi. Anan Annabin Allah ne yake ambatawa cewa 'yan uwanSa zasu kulla masa wani munmunan makirci, Makircin Mata kuma Azizu Misra ne ya ambata. Sannan makircin Mata soyayya ce, makircin Maza kuma kisa ne da ta'addanci. Don makircin da Annabi Ya'aqub (Alaihissalam) ya jiwa danSa tsoron sa shine yazo a gaban wannan Ayar, ga abinda 'yan uwanSa suke cewa:- ﭐﻗﺘﻠﻮﭐ ﻳﻮﺳﻒ ﺃﻭ ﭐﻃﺮﺣﻮﻩ ﺃﺭﺿﺎ * Ku kashe Yusuf ko kuma ku jefashi a wata kasa me nisa (ta yadda zai yi nesa da mahaifinSa). Karshe sai suka yi matsaya akan su jefashi a cikin rijiya suka ce:- ﺃﻟﻘﻮﻩ ﻓﻰ ﻏﻴﺎﺑﺖ ﺍﻟﺠﺐ * Ku jefashi a cikin duhun rijiya. Wannan shine kaidin Maza, hassada, kyashi, kiyayya, munafunci da sauran su, amma kaidin Mata soyayya ne. Don haka anan bawai ina cewa Mata basa da kaidi bane, a'a shi kaidi da makirci ana iya samunSa daga bangaren Maza da Mata, to amma duk lokacin da kaga an samu kaidi daga mata to zaka gan yana da alaka da soyayya, imma ta kulla kaidi ta hana mijinta karin aure ko ta kulla kaidi ta kori kishiyarta ko ta kullawa saurayi kaidi sbd yace baya sonta ko ta kullawa saurayi kaidi sbd ya rabu da ita a bisa wani Dalili ko a ganin damanSa ko ta kulla kaidi akan wani abu makamancin hakan, amma dai idan kayi nazari sai kagan kaidin yana da alaka da soyayya ga Namiji da son zama ita kadai a wurinSa, sabanin kaidin Maza da yake Munafunci ne, da hassada, da kiyayya, da kyashi wanda wasu lokutan suke kaiwa ga ta'addanci, shiyasa idan kana bibiyan ayoyin Alkur'ani mai girma zaka gan a galibi duk inda aka ambaci kaidin Maza sai ka samu ya hadu da ta'addanci a ciki. Don haka cewa kaidin Mata yafi na shedan wannan kazamar kalma ce, inama jin tsoron kalmar tana iya sa ka kafirta, don haka mu nesanci furta irin wannan kalmar. Allah ya mana afuwa baki Daya. Copied