Talaka BAWAN ALLAAH

Talaka Bawan Allah
Jiya bayan magriba naje unguwar Kurna a Kano dai-dai inda na tsaya a bakin titi akwai masu saye da siyarwa, sai na bukaci na sai pure water domin jika makoshi ina zuwa sai naga wani dan karamin yaro da robar ruwansa na dauko N 100 nace "ruwa nake so guda daya' yace "bashi da canji".
Har na tafi sai na dawo na yiwa yaron tambayo yi shekarun sa bakwai (7) mahaifinsa ya rasu dan makarantar primary ne amman yace min a sati sau biyu ko sau uku yake zuwa saboda shine babba a wajen mahaifiyarsa yana fafutukar nema musu na garin kwaki.
Ba'a maganar makarantar Islamiyya sannan a bokon kwakwalwar yaron tana tafiya sosai bisa tambayo yin da na yi masa.
Jarinsa na ruwa N 80 ne a haka yake gudanar da rayuwar sa, kayan jikinsa duk sun yayyage takalminsa ya side sosai.
Na dauki N 200 nace kanina ka kara jari ka kuma dinga rokon Allah sannan in ka samu lokaci ka dinga zuwa makarantar, sannan kace ayi kokari ka samu Islamiyya ita ma ka dinga zuwa.
Muka yi sallama na tafi abin na damuna a raina.
Wai anya kuwa 'yan uwa muna tallafawa marayun dake yankinmu kuwa?
Ko kuma mun bar aikin sai iya na wadansu tsiraru ne?
Yanzu don Allah yaya kuke kallon rayuwar Wannan yaron anan gaba?
Yanzu idan aka ce a unguwa da marayu ace ni da kai muna dan tallafa musu da abinda bai taka kara ya karya ba shin ba za'a rage wannan zafin radadin ba?
#BasheerSharfadi Sharfadi.com

Post a Comment (0)