SHARHIN FIM DIN MY NAME IS KHAN

Takaitaccen sharhi akan film din MY NAME IS KHAN.
Film ne wanda akayi shi a 2010,kuma Alhamdulillahi ya sami karbuwa sosai,tunda har sai da yafi dukkan wani film tsada kuma akafi siya a masana'antar Bollywood,film din ya kawo kimanin Crore 100 .
Mai bada umarni na wannan film shine Karan Johar,sai kuma wa'yanda suka shirya sune: Hiroo da Gauri khan. kamfanin da suka dauki nauyin wannan shiri sune: Dharma production,Red chillies entertaiment da kuma Fox star entertaiment.
Jaruman shiri sune: Sharukh khan,Kajol,Sonya jehan,Jimmy Shergill,Zarina Wahab,Arjan Aujla,Arjun mathur,da sauransu.
Shirin anyishine kan wani tsaka-tsakin iyali,wato Rizwan,Zakir da kuma mahaifiyar su Raziya khan. Shi rizwan an haifeshi tare da matsala,kansa yana rawa,sannan da yanayin yafiyar sa,amma Ubangiji yayi masa baiwa na fahimtar abubuwa da sauri,duk da matsalar da yake da,mahaifiyarsa bata gazaba gurin nuna soyayyarta agareshi,har ta kai ga dan uwansa bayajin dadi. Akwana a tashi,sai shi zakir ya sami fita kaqar waje karatu,acan ya girma,har yayi aure,sunan matar shi Haseena,sannan yana aiki acan,anan ana nan,sai Allah yayi wa mahaifiyar su mutuwa,sai Rizwan ya koma can gurin dan uwansa da zama,har ma ya fara aiki da shi Zakir din
Yana kan yin aikin ne,sai ya hadu da Mandira,haduwar tasu ke da wuya,suka zama abokanan juna,daga nan sai soyayya ta shiga tsakanin su,sai dai ita mandira tana da yaro daya(Sameer) wanda ta haifa da tsohon mijin ta,ana nan sai soyayyar tasu takai da har sun yi......
. Soyayyar tasu takai da har sunyi aure,sai dai shi sameer bai so hakan ba,to azaman da sukai ne,shi Sameer ya ga baiwar da Allah yayi wa Rizwan,sai ya saki jiki dashi suka saba sosai,suna cikin zaman su mai dadi cike da farinciki,kwatsam sai watarana a makarantar su Sameer,ya sami matsala da wasu yan makarantar,har ta kai da shi Sameer din ya rasa ransa,nan fa matsala ta afku tsakanin Mandira da Rizwan,har ita Mandira ke cewa Rizawan,ba wani abu bane dalilin mutuwar danta face Wannan suna da danta ke amfani dashi a karshen sunan sa wato KHAN,kuma shi Rizwan danta'adda ne,tunda hakane yanzu ba ita ba shi,har sai yaje America ya gayawa shugaban America cewa sunan shi KHAN,kuma shi ba dan taadda bane.
Rizwan ya shirya ya kama hanyar sa ta zuwa america don tabbar da cewa shi ba danta'dda bane,akan hanyar tashi ya hadu da jarabawa iri iri,duk da haka ya jure yayi hakuri,domin ya cinma burinsa na bayyana cewar shi mutum ne na gari,har zaman kurkuku yayi,ya kuma hadu da mutane daban-daban,don har sai da ya kusa rasa rayuwar sa.
Akarshe dai ya samu daman cika burin sa,tare da taimakon wasu mutanen kirki,ya kuma tabbatar wa da shugaban kasa cewa sunan sa KHAN,kuma shi ba dan ta'adda bane,sannan Addininsa bai yarda da duk wani ta'addanci ba,daga bisani shi kansa shugaban kasar America ya sake tabbatar wa Rizwan cewa sunan sa KHAN,kuma shi ba dan ta'adda bane.
Sannan ita Mandira,tai farinciki,da nuna nadama tare da bawa Rizwan hakuri,suka koma suka ci gaba da zaman su na soyayya tare da cikakken farin ciki.
Taqaitaccen sharhi kenan akan film din MY NAME IS KHAN.
*NAKU AKODA YAUSHE*
*IKRAMKHAN VEERON KE VEER* WUSASA ZARIA.
*KADUNA URDU KI FANS ZINDA BAAD!*

Post a Comment (0)