SHARHIN FIM DIN VEER-ZAARA

Sharhin Fim Din Veer-Zaara a takaice
Veer-Zaara Fim Din soyayya ne da akayi a 2004 kuma Yash Chopra ne ya bada umurnin Fim Din karkashin Kamfanin Yash Raj Films. Akwai Jarumai a cikin Fim Din irinsu Shahrukh Khan, Preity Zinta,
Rani Mukherji, Manoj Bajpayee , Kirron Kher, Divya Dutta, Boman Irani,
Anupam Kher, Amitabh Bachchan da kuma
Hema Malini. Aditya Chopra ne ya rubuta labarin Fim Din.
Labarin ya fara ne a 2004, lokacin da Gwamnatin Pakistan ta yanke hukuncin duba irin halin da Fursunonin India suke ciki. Saamiya Siddiqui, wacce Matashiyar LAUYA ce a Pakistan sai ta zamo mai kare Fursuna mai lamba ta 786. Fursunan wanda ya bayyana sunan sa a matsayin Veer Pratap Singh, yaki yiwa kowa magana har na tsawon shekaru 22. Bayan ta matsa masa ne sai Veer ya baiwa Saamiya labarin sa.
Zaara Haayat Khan, 'Yar Gidan wani fitaccen dan siyasa ne a Lahore, kafin Mutuwar kakar ta mai suna Bebe, ta roki Zaraa da ta cika mata Burin ta na karshe a duniya wanda shi ne ta watsa tokar gawarta a kogin Sutlej kamar yadda aka yiwa kakannin ta.
A hanyar ta na zuwa India ne motar Zaara take ciki ta gamu da hatsari Veer, wanda sojan sama ne shi ne ya cece ta, kuma da taimakon sa ne ta samu har ta cika Alkawarin da ta dauka. Daga nan sai Veer ya roki Zaara kan cewa ta biyo shi zuwa kauyen su ta kwana koda daya ne Kasancewar za'a yi bikin Lohri.
A can ne suka gamu da kawun Veer u Choudhary Sumer Singh da gwaggon sa Saraswati Kaur. Kawun nasa ya ce mishi ya gani a mafarki an nuna masa Veer ya auri Zaara. Daga nan Veer ya fahimci cewa ya kamu da son Zaara.
Washegari sai ya raka ta tasha domin ta hau Jirgin kasa a Lahore, Veer na shirin bayyana mata abinda ke ranshi kenan sai ga wanda zai auri Zaara yazo,dama neman ta yake. Gab da zata hau Jirgin ne Veer ya bayyana mata yana son ta, saboda cikin sauri ne, Veer sai ya kasa Fahimtar ko itama tana son shi ko A'a. a sannan ne kuma ya fahimci cewa daya daga cikin awarwaron kafar ta yana tare da shi, amma sai tayi mishi alamar ya rike. Dukkan su sunyi tunanin ba zasu kara haduwa ba.
Bayan sun isa Pakistan, sai Zaara ta fahimci cewa ta kamu da Matsanancin son Veer, sai dai kuma ya zama Wajibi a gare ta auran wanda aka sa musu rana tare domin yin hakan zai karawa babanta karfin iko a harkar siyasar sa. Amma sai ta fadawa mahaifiyar ta cewa akwai wani dan Indiya fa wanda zai iya Sadaukar da rayuwar sa domin ta, kuma gaskiya ta kamu da son shi. Amma sai mamanta ta nuna bacin ranta da wannan labari, daga nan sai ta fadawa 'yar aikin su kuma kawar ta mai suna Shabbo irin son da takewa Veer. Shabbo sai ta kira Veer sannan ta roke shi da ya dauke Zaara su gudu India.
Veer wanda dama can ya fadawa Zaara cewa zai iya Sadaukar da rayuwar sa saboda ita, sai ya bar aikin sojan nasa ya tafi Pakistan domin ya dawo da ita India. Amma sai mahaifiyar Zaara Mariyam Hayaat Khan,ta roke shi da ya tafi ya bar Zaara saboda Mahaifin Zaara, Jehangir Hayaat Khan babban dan SIYASA ne, kuma aikata hakan Barazana ce ga kimar sa da kuma lafiyar sa in har yaji wannan labarin.
Veer sai ya karbi wannan uzurin sannan ya yanke hukuncin komawa gida, amma sai Raza, wanda ransa ya gama baci da Zaara tayi mai sai ya kala wa Veer Sharri wai shi dan leken asirin India ne, hakan yasa aka kama shi aka kaishi gidan yari.
Yayinda Veer ya gama baiwa Saamiya labari, sai ya bukaci kada ta fadi sunan Zaara ko iyalan ta a yayin kare shi. Lamba ta 786 lamba ce da Musulman Pakistan suke girmama wa sosai, hakan yasa Saamiya tayi tunanin duk yadda aka yi Allaah na Nufin Veer da Alkhairi ne, don haka sai ta yanke Shawarar zuwa India domin samo shaidar da zata kare Veer.
Yayinda Saamiya taje can kauyen su Veer sai ta tarar da Zaara da Shabbo, ashe sun baro Pakistan sun dawo India domin kula da karatun yara mata Kasancewar kawun Veer shi da matar sa sun mutu. Zaara tayi tunanin Veer ya mutu a hatsarin motar da akayi wacce ta kashe kowa bayan ta ko ne. Saamiya sai ta tafi da Zaara Pakistan domin ta wanke Veer a kotu, Kotun dai ta saki Veer tare da bashi hakuri a madadin Pakistan. Fim Din ya kare ne Yayinda Veer da Zaara suke bankwana da Saamiya a kan Iyakar Pakistan domin Komawa kauyen su Veer.
Saratu Mastani

Post a Comment (0)