SHAWARA TA A GARE KI

SHAWARA TA A GARE KI!
Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu.
Ina Fatar Wannan Sakon zai isa gareki a duk inda kike.
Yake 'Yar Uwa ta, Kada Ki yarda baqin ciki ko tashin hankalin rayuwa su dagula miki tunanin ki ko tsarin rayuwar ki.
Kada ki yarda Talauci ko rashin samun abinda kike fatar samu yasa Imanin ki yayi rauni.
Kada ganin Qawayen ki, ko Sa'o'in ki suna saka Gayan da ke bakya sakawa, ko suna shafa man da ke bakya Shafawa, ko suna Fesa turaren da ke bakya Fesa irin sa ko kuma suna wani abu makamancin hakan wanda ke ba kya yi yasa ki manta da irin tarin baiwa da Ni'imar da Allaah Subhanahu Wata'ala Yayi miki har kisa kanki a cikin Damuwa.
Kada ki ga wata wai don tana da Farrar Fata, dogon gashi ko hanci, dogayen kafafu ko kuma kayan dirin jiki hakan yasa ki dinga jin kunya ko nauyin fita ko yin mu'amala a yayin da kuke tare, kuma kada wadannan abubuwan su ja hankalin ki har akai matsayin da zaki dinga mata biyayya fiye da qima.
KI sani cewa kema Kyakkyawa ce, kuma kema abar so ce ga wasu (In ma ba ga kowa ba), kuma kema mace ce don haka kada wani abu na rayuwa yasa ki manta da wannan.
Babu Mamaki idan na ce miki kema Kyaykkyawa ce ki qi Amincewa da hakan, amma ina so ki sani cewa; Kowane Mutum yana da masoya, haka ma Makiya, kada ki taba tunanin baki da Masoyi kuma kada ki taba tunanin cewa ke Mummuna ce sannan kuma kada ki taba tunanin baki da makiya. Sannan ina so ki sani cewa "Kowane Mutun Kyakkyawa Ne a idon Masoyan sa, Kuma kowane Mutum Mummuna ne a idon Makiyan sa." Lallai Kema Kyakkyawa ce Domin Allaah baya taba halittar Mummunar Halitta, Lallai Allaah Yana Da DALILIN SA na Halittar ki a yadda kike, Matukar ba kin Raina irin Ni'imar Da YA Yi miki bane, to Ki karbi kanki a bisa irin matsayin da kika tsinci kanki a ciki kuma ki nemi Dacewar sa. Lallai SHI mai Amsa ADDU'AR bayinSa ne.
Amma fa lallai ne sai kinyi hakuri, kuma sai kin jure. Lallai Allaah Yana Tare da masu Hakuri.
Raees Assalafy
©2017

Post a Comment (0)