BABU ADDININ DA YA AMINTA DA ZUBAR DA JININ DAN ADAM BABU DALILI

*BABU ADDININ DA YA AMINTA DA ZUBAR DA JININ DAN ADAM BABU WANI DALILI!* _A Bisa Wannan Ne Yau Alhamis 10/05/2018 Munka Taru Waje Daya munkayi Zanga-zangar Lumana Domin Nuna Adawarmu A Fili Akan Mutanen Karkarar Da Ake Yiwa Kisan Gilla Babu Gairan Babu Dalili, So da Yawa 'Yan Uwanmu A Cikin Kauyuka Suna Rayuwa Cikin Fargaba Yanayin Firgici, Domin Suna Tunanen Kowane Lokaci Za'a iya Kai Musu Hare-haren Ta'addanci._ _Rayuwar Talakan Karkara Tana Da Matukar Amfani Ga Manyan 'Yan Siyasarmu, Domin Har A Cikin Karkarar Ake Isko Su Wajan Yakin Neman Zabe, Amma Daga Baya Gwamnati Ta Kasa Kare Rayukansu Da Dukiyoyinsu Bayan Ta 'Dare Madafun Iko._ _Wannan Dalilin Yasa Munkayi Gan-gamin Zagaye domin Roko Ga Gwamnatin Jihar Zamfara Data Dubi yuwuwar Lunkawa Akan Kokarinta, Domin Ganin Komai Yazo Karshe, Domin Saida Zaman Lafiya Sannan Jiha Take Ci Gaba Wajan Al'amurran Yau Da Kullum._ _Muna Addu'ar Samun Zaman Lafiya Mai 'Dorewa A Jihar Zamfara Dama Kasa Baki Daya_ # Stopkilling_In_Zamfara ~Nura Muhammad Mai Apple Gusau~

Post a Comment (0)