*_TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA??_*
*Tambaya*
AssalamuAlaikum. Mallam inna da tambaya ? Yaya hukuncin Matar da miji ya bukacheta sannan tana Azumin sunna. Ta ki ta Aminche mishi
*Amsa*
Wa'aleikum assalam, ta yi kuskure ya kamata ta amsa kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko da babu dalili, Annabi ﷺ yana cewa "Mai azumin nafila sarkin kansa ne in ya Ga dama ya cigaba da azumin, in kuma ya so ya karya "kamar yadda Tirmizi ya rawaito a Sunan.
Allah ne mafi sani.
30/1/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.