Tafiya Muke Babu Makawa Sai Mun Je

*_TAFIYA MUKE BA MAKAWA SE MUNJE!!!_*

_Aljannah ko wuta? Allah kasa muna aljannah*_

*_Yan uwa Musulmai kamar yau ne muke cewa saura kwana kaza azumi, Yau gashi har munkai rabi._*

_Shin muna tuna cewa kullum idan muka waye gari ana turamu ne zuwa ga  kabari ana nade duniyar mu.??_

_Da yawa daga mutane sunyi burin su hallaci wannan wata amma Allah ya karbi rayukansu,da yawa sunyi burin ganin wannan wata se gashi suna kwance babu lpy, yakai dan uwa Allah ya baka lpy wannan baiwace wadda ya zama dole mu godewa  Allah._

*_Ya kai dan adam kana taka kasa da kafarka watarana fa cikinta zaka koma,amma kasan irin takun da zakai mata._*

*Wucewar dare da rana yana tinawa magabata izna da tinawa da Allah.*

*_Wani mai hikima yana cewa babu wani abun farin ciki kasan cewar kullum idan an wayi gari ana tafiya izuwa ga Allah._*

*_Fudail ibnu iyaad, ya tambayi wani mutum yace shekarunka nawa? mutumin yace 60,se fudail yace to kasani kana daf da isa zuwa ga Allah, se mutumin yace innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, se fudai yace kasan ma'anar abunda kace? yace a'a, yace kace ni bawan Allah ne kuma garesa zaka koma._*

*Dan haka mu sani ga Allah zamu koma kuma mu shiryawa tambaya.*

_Abu Huraira yayin da yazo mutu se yake kuka,aka ce meyasa kake kuka? yace karancin guzirina ga hanyar tanada nisa gata da kwazazzabai ga tudu a gabana da zan hau, ina na gangaro Aljannah ce ko Wuta, idan Abu huraira zai fadi haka ina gani dakai dake?_

*_Wanda kullum se ance Allah ya yarda dashi._*

_Musani a wannan wata kullum Allah yana yanta bayinsa a wannan wata,yakai mawadace debo ka bayar, ya kai dan kasuwa manya da kanana sassauta, yakai malami yi kira zuwa ga Allah yakai dalibi dage da karanta qur'ani,dage da tsayuwar dare._

*_Domin samun dacewa._*

_Yakai dan uwana talaka kaima kanada abin da zaka ciyar manzon Allah (SAW) yace kyakyakyawar kalma sadaka ce hani ga mummuna sadaka ne umarni da kyakyakyawa sadaka ne._

_yan musani Allah mai jin kaine fiye da yadda iyaye ke jin kan yayansu,yazo a hadisi daga Umar yace wata an kawowa manzo ribatattun yaki,wata mata tazo tana neman danta ta dakkosa ta bashi mama yasha manzon Allah yace kina ga zata iya jefa dan nan nata wuta? sukace a'a, mazon Allah yace Allah yafi jin kan bayinsa fiye da yadda taji kan danta._

_Mafita yan uwa shine mu koma ga Allah domin allah na cewa._

_Allah baya canzawa bayinsa  halin da suke ciki matukar basu canzawa kansuba._

_Sannan kyakykyawa tana tafiyar da mummuna._

_Allah kasa kyawawan ayukan mu su rinjayi munana ameen_

_Sannan musaka kasarmu a addu'a mai kyau da shuwagabannin mu, domin shiryiwarsu samun saukin mune idan kullum muna la'antarsu kara lalacewa zasuyi._

*_Manzo (SAW) Yana cewa ka fadi Alkhairi ko kai shuru._*

            *_Faisal Nasir Muhammad_*
*GABATARWA ASIYA IBRAHIM BAWA*

Post a Comment (0)