TAKAITACCEN TARIHIN JARUMI HRITHIK ROSHAN
Hrithik Roshan Jarumin Fim Din India ne wanda yake fitowa a Fina Finan Bollywood. Yana daya daga cikin Jaruman Fina Finan India Wadanda Suka FI tsada wajen biyan su kudi kafin suyi aiki. Jarumi ne da ya Shahara musamman a fagen rawa da kuma iya fada.
An haifi Hrithik ne a ranar goma ga watan Janairu Shekara ta Alif dubu daya da dari tara da Saba'in da hudu (10th January 1974) a Maharashtra, Mumbaai dake kasar India. Mahaifinsa Shi ne Furodusa Kuma Darakta Rakesh Roshan, shi Kuma Rakesh Roshan DA ne a wajen tsohon Mai bada Umurni a fannin Wakoki da kidan nan wato Roshanlal Nagrath. Mahaifiyar sa kuma sunan ta Pinky, ita kuma 'Ya ce a wajen Wani Furodusa Kuma Darakta Mai sun J. Om Prakash. Sannan yana da wani kawo mai suna Rajesh wanda shi kuma Makadi ne. Hrithik yana da wata yaya guda daya mai suna Suna ina. Jarumin Yana da Jibi da' Yan Bengali ta hanyar Kakarsa amma shi yana bin Addinin Hindu ne wato Hinduism.
Hrithik Roshan ya sha fama sanda yake karami sakamakon an haife shi da abinda Bahaushe yake kira da "Cindo", wato wani yatsa ne ya fito a jikin babban yatsan shi na dama ya hade da dayan. Wannan ne yasa da yawan abokan karatun sa suke kaurace masa. Bayan haka kuma, Jarumin ya kamu da lalurar In Ina tun yana dan shekara shida a duniya, wanda hakan ya haifar mishi da matsala sosai har takai cewa idan za'a Jarabawa wace ta jibanci magana yakan yi karyar bashi da lafiya domin ya kaucewa Jarabawar.
Kakan sa, Om Prakash shi ne ya fara fito da shi a cikin Fim lokacin yana dan shekara shida a cikin wani Fim mai suna Aasha wanda aka yi a 1980 inda ya taka rawa a wata Waka dake cikin Fim Din. Kasancewar Ya taso ne a gidan masu shirya Fim, Jarumin ya fito a cikin Fina Finan da gidan su suke shiryawa daban daban irin su Aap Ke Deewanee, Aas Paas da dai sauransu. Sai dai Fim Din da ya fara fitowa a ciki har yayi magana shi ne Bhagwaan Dada a lokacin yana da shekaru 12 a duniya. A wannan lokacin ne Hrithik Roshan ya bayyana Ra'ayin sa na son ganin ya zama cikakken dan Fim, amma sai baban sa ya hana shi yace ya dage da karatun sa kawai.
Yayinda Ya Fara Zama Matashi, Jarumin ya gamu da Lalurar Scoliosis wacce bayan anyi Gwaje Gwaje aka ce cutar ba Zata barshi yayi rawa ko fada ba a Fim. Amma saboda naci, sai Hrithik Roshan ya yanke Shawarar shi dai zai zama jarumin Fim ko ma ta yaya ne. Shekara daya da yin wannan gwaji, sai Hrithik ya fara Dan yin guje guje a bakin teku yana dan motsa jini. Kuma ya zamana yanayin hakan ba tare da fuskantar wata matsala ba. Daga nan ne sai ya fara kara nisan gudun nasa har dai ya zamana yana iya yin komai ba tare da wata matsala ba.
Hrithik yayi karatun sa ne a Sydenham College, inda bayan karatun sa, yana kuma yin duk wasu abubuwa da suka shafi Raye-Raye Da Wake-Wake a makarantar, daga karshe dai ya kammala karatun sa a fannin Cinikayya wato Commerce. Hrithik ya Taimaki Mahaifin sa Rakesh Roshan a cikin Fina Finan sa guda 4 sune KHUDGARZ, KING UNCLE, KARAN ARJUN DA KUMA KOYLA, Yayinda a hakan kuma yake share wurin yin Fim Din tare da Rabawa Ma'aikatan Fim Din Shayi. A duk lokacin da aka kammala wani bangare na Fim Din Koyla, sai Hrithik Ya zo gefe yana Kwaikwayon irin Yadda Shah Rukh Khan Yake yi a Fim Din domin yaga yaya zai yi in shima ya tsinci kan sa a matsayin Jarumi. Bayan Taimakon Mahaifin sa da yake yi, Hrithik ya koyi yadda ake shirin Fim a wajen Kishore Namit Kapoor .
Da Fari, Hrithik an so ya fara fitowa a cikin Fina Finan India a matsayin Jarumi ne tare da Preity Zinta a Cikin Fim Din Shekhar Kapur Tara Rum Pum. Maimakon hakan sai ya fito a cikin Fim Din Baban sa mai suna KAHO NAA PYAAR HAI a 2000 Tare da Sabuwar Jaruma Ameesha Patel.
Saboda ya shiryawa Fim Din, Hrithik sai da ya samu Horo ta hannun Jarumi Salman Khan domin ya Gina jikin sa, kuma sai da ya dauki Darussa na musamman a bangaren rawa, Waka, tuki, hawa katanga da Makamantan su. Fim Din ya samu Karbuwa sosai Yayinda shi ma Jarumin ya sha Yabo a wajen 'yan kallo da masu sharhin Fina Finai tare da samun lambobin Yabo da dama.
Fim Din sa na biyu kuma shi ne FIZA inda ya fito tare da Karisma Kapoor da Jaya Bachchan a cikin sa. Shima wannan Fim yayi kyau dai dai Gwargwado kuma an yaba da irin aikin jarumin. Fim dinsa na gaba kuma shi ne MISSION KASHMIR inda ya fito tare da Sanjay Dutt, Preity Zinta da kuma Jackie Shroff, shima wannan Fim ya kawo kudi sosai kuma anyi nasara wajen fitar da shi.
A shekara ta 2001, Hrithik yayi wasu Fina Finai guda biyu, na farko dai shi ne YAADEIN inda aka hada shi da Kareena Kapoor da kuma Jackie Shroff. Sai Kuma Fim Din KABHI KHUSHI KABHIE GHAM inda aka hada shi da Amitabh Bachchan, Shah Rukh Khan, Jaya Bachchan, Kajol da kuma Kareena Kapoor. Duka Fina Finan sunyi kyau, sai dai masu sharhi sun kushe YAADEIN saboda wasu dalilai, yayin da KABHI KHUSHI KABHIE GHAM ya samu gagarumar nasara.
A shekara ta 2002 jarumin ya sake haduwa da Ameesha Patel a cikin Fim Din AAP MUJHE ACCHE LAGNE LAGE wanda duk da yayi kyau amma bai taka wata rawar kirki ba a Akwatin kawo kudin Fina Finan India. Daga nan kuma sai yayi Fim Din NA TUM JAANO NA HUM wanda shima dai bai taka wata rawar kirki ba. Fim dinsa na gaba daga nan shi ne MUJHSE DOSTI KAROGI tare da Rani Mukerji da Kareena Kapoor. Shi kam wannan ya kawo kudi a kasashen waje, amma shima bai tabuka abin Arziki a gida ba. Daga kuma yayi Fim Din MAIN PREM KI DIWANI HOON wanda shima dai sai a hankali.
Nasarar Jarumi Hrithik Roshan ta dawo da karfin ta ne bayan ya fito a cikin Fim Din Baban sa mai suna KOI MIL GAYA inda aka hada shi da Preity Zinta. Wannan Fim ya samu gagarumar nasara kuma ya dawowa da jarumin Martabar sa tare da wasu lambobin Yabo ma. Fim dinsa na gaba shi ne LAKSHYA inda ya sake fitowa tare da Preity Zinta a cikin sa. Daga nan bai sake fitowa a wani Fim ba sai a shekara ta 2006 inda yayi fitowa ta musamman a cikin Fim Din I SEE YOU.
Sai dai kafin nan ya fito a Cikin Fim Din KRRISH tare da NASEERUDDIN SHAH da Kuma Priyanka Chopra. Yaci bakar wahala a wannan Fim Din domin sai da ya karya yatsu guda biyu yayi daukar Fim Din, babban yatsar hannun sa daya da kuma na kafa daya. Sai dai wannan wahala bata tashi a banza ba, domin krrish ya karbu sosai kuma ya kawo kudi kimanin DALA MILIYAN 18 a duniya baki daya.
Daga nan sai Fim Din DHOOM 2 Inda ya fito a matsayin shahararren barawo tare da Aishwarya,
Bipasha Basu, Uday Chopra da kuma Abhishek Bachchan. Shima wannan Fim ya karbu sosai kuma ya kawo kudi Kimanin DALA MILIYAN 24 a duniya baki daya tare da samarwa jarumin lambobin Yabo. Jarumin yayi fitowa ta musamman a cikin Fim Din OM SHANTI OM tare da Jarumai da dama.
Daga nan ne ya ci gaba da Jagorancin manya manyan Fina Finai tare da yin fitowa ta musamman a cikin wasunsu. Daga cikin irin wadannan Fina Finan akwai
Jodhaa Akbar
Luck by Chance
Kites
Guzaarish
Zindagi Na Milegi Dobara
Don 2
Agneepath
Mohenjo Daro
Krrish 3
Bang Bang! ,
Kaabil
Akwai kuma wasu Fina Finan sa da zasu fito kamar haka:
Super 30 25 January 2019
Akwai wani Fim Din sa da Tiger Shroff karkashin Kamfanin Yash Raj Films wanda ba'a saka masa suna ba tukun amma zai fita a January 2019
Krrish 4 kuma da KIRSIMETIn 2020.
Hrithik yayi ma Kamfanoni da dama tallan Hajojin su, daga cikin Kamfanonin akwai Coca-Cola , Tamarind, Hero Honda, Provogue , Parle Hide and Seek, Reliance Communications da dai sauransu.
A ranar 20 December 2000, Hrithik Roshan Ya auri
Sussanne Khan a Bangalore. Duk da cewa Addinan su ba daya bane (Shi Hindu Ita Musulma) yace ya na matukar girmama Addinin ta kamar yadda yake girmama nashi.
Yana da Yara guda biyu, Hrehaan (an haife shi a 2006) Hridhaan (an haife shi a 2008). Sun rabu da matar tasa s Disamba 2013 Yayinda sakin kuma ya tabbata a Nuwamba 2014.
Hrithik Roshan yayi Yunqurin daina Fim a 2000 lokacin da wasu 'yan bindiga dadi suka kaima Baban sa Hari.
Yana matukar kokarin ganin ya koyi duk wani abu da ya shafi Fim Din da zai fito a ciki kuma yana fada da kanshi ne a cikin kowane Fim dinsa (Ma'ana babu choge)
A shekara ta 2006, Hrithik Roshan yana daya daga cikin Jaruman Bollywood guda 4 wadannan da akayi butum butumin su a United Kingdom Karkashin sunan BOLLYWOOD LEGENDS, sauran sune Priyanka Chopra, Kajol day Shah Rukh Khan.
An hada wani katon butum butumin sa wanda aka aje a gidan Tarihin
Madame Tussauds dake Landan a January 2011, wanda hakan ya maida shi daya daga cikin Jaruman Fina Finan India guda 5 da aka yi musu irin hakan.
Jarumin ya samu Lambobin Yabo masu yawa daga cikin su akwai lambobin yabon Filmfare guda 6, 4 daga cikin su a matsayin jarumin Jarumai, kuma yana da Dimbin Kudi a banki fiye da kowane Jarumi a India.
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com
Tags:
Fina-Finai (Films)