SHAWARA ZUWA GA MALAMAI DA GWAMNATI

Shawara zuwa ga malamai da government...
1). Yakamata a bude islamiyya duk namijin da zaiyi aure lalle sai yaje makarantar dan samun ilimin zaman takewar aure tsakanin da matarsa. Ya zama har sai ya nuna certificate alamun yayi Kafin a bashi auren yarinya.. Dalili;: duk mijin daya wadata da ilimin addini nutsuwa tana ratsa zukatansa kuma Bazaiyi aure cikin jahilci ba, anason duk Inda shugaba yake yazama Mai riko da addini, sannan duk wannan shiririta da ake Kafin aure da lokacin Biki e.g pre wedding pictures dasu dinner maza da mata shaidan tun farkon aure yayi Kane Kane. Amma indai da ilimi toh fa wani abun zai ragu, sakin aure ma zai ragu kuma matar ma nutsuwar mijin zata koya ta bishi yadda yake so tun farko.
2). Duk namijin da ya bukaci Karin aure sai ya tabbata matarsa ta gida ta wadata,, kuma zai iya tsare mutuncin amaryar da Uwargidan batare daya sasu a kuncin rayuwa ba. In da hali a tabbatar da ya canjawa Uwargida Kayan daki Dana kitchen da na sawa saboda kar a samu Raini a gidan sa,,
Dalili;: zafin kishin Uwargida zai ragu zata gane cewa mijinta har yanzu yana sonta bazai gujeta ta, sannan amarya itama bazata raina Uwar ba zasu zauna lafiya. Dan idan haka na faruwa wata matar ma Allah Allah zatayi mijin ya Karo aure. 😜
3). Malamai su daure dayima maza nasiha akan wayarsu, yawan chatting da Matan banza bashi da amfani, idan da yarda,so da kauna meye dan matarka ta taba wayarka. Idan namiji baya yawan danna waya babu matar da zata damu da wayar miji,, wasu mazan har toilet da wayarsu suke zuwa, dole matarsa taji saitaga meye a ciki,, babu dalilin da za'a ce mace bazata taba wayar miji ba shima ya taba tata inba dai yasan da wani abu daya kaucewa Shari'a.. Idan akace ba taba waya an basu damar ajiye Komai ma dayin sharholiya zargi kuma ya shiga tsakani, aure kuwa da zargi babu amfani.
4). A yawaita tunatar dasu wadata iyalin su, da bawa matansu hakkin su,, dan yanzu majority of Gidajen auren hausawa Akwai problem.. Kuma duk problem din maza ke kirkiro Shi, ko Suki Sutura ko Suki bada abinci isheshshe kuma su bazasu zauna a gida time to time ba da Iyali kullum suna yawo sai Kowa yayi bacci zasu shigo Kamar barayi, kuma a dawo ko mace tayi kwalliya Baza'a kalleta ba Saidai a kalli waya,, ina zaman lafiya...
Idan Baza'a gyara ba maza su dawowa da mata martabarsu toh yanzu mata suka fara daukar hukunci a hunnun su..
A daure ayi forward plzzzzz.
Sign
Daga kungiya

Post a Comment (0)