WANNAN KASON AKWAI SON ZALUNCI

WANNAN KASON AKWAI Zalunci !!!
.
Karatun boko....
.
Da sassafe mun tashi anyi wa yara wanka, an haɗa musu shayi mai kauri sun sha, an sanya musu uniform na boko wankakku gogaggu, ga turare mai qamshi, ga takalmi mai igiya, yara gwanin ban sha'awa, ga taliyar indomie an dafa an lulluɓe ta da soyayyen ƙwai, an zuba a cooler an sanya a kwando, ga ruwa ko wani dai kalar soft drinks.
.
Cikin lokaci an ɗauki yaro a abin hawa mota/babur, an kai shi makarantar boko tun ƙarfe 7:30am na safe, ba za'a taso su ba sai qarfe 2:00pm ko 3:00pm idan ranar babu lesson kenan. In ko da kwai se 4:00pm wasu ma se 5:00pm,
.
Idan lokacin biyan kuɗin mkrt (School fees) yayi, ka ga cikin lokaci an biya maƙudan kuɗaɗe ba tare da wani ɓata lokaci ba, kuma banki ma zaka je ka biya sai dai ka kawai ka kawo teller makarantar a baka reciept.
.
Islamiyya....
.
Idan an dawo daga boko qarfe 2:00pm ko 4:00pm, yaro ya dawo a gajiye yana jin barci, a lokacin ne za'a dinga neman uniform ɗin islamiyya a lungu da saƙon ɗakin, a hango rigar ƙarƙashin kujera, wandon a gan shi da ƙyar a kitchen ko ƙarƙashin gado, jakar makarantar kuwa da ƙyar za'a gano ta a wani lungu, kafin a nemo inda littattafan suka shiga, kafin dai kammala tattaro kayan sai wurin 4:30pm zuwa 5:00pm.
.
Sannan ne za'a kora yaro yana kuka cikin mummunan yanayi haka zai tafi islamiyyar.
.
Biyan kuɗin makaranta abinda baya wuce ₦500,ko wani me kama da haka kuwa a wata, sai a kwashe watanni ba'a biya ba, idan an koro yaron sai iyayen su ce zauna a gida abin ka in wata ya yi nisa sun gama karɓar ka koma, haka yaro ze ta shiririta a wata bai wuce samun karatun sati ɗayaba.
ANYA WANNAN TSARI ZAI HAIFAR DA ƊA ME-IDU KUWA ?
MU tuna SHUGABA (salla-llahu alaihi wa sallama) yana cewa:
(( ﻛُﻠُّﻜُﻢْ ﺭَﺍﻉٍ ﻭَﻛُﻠُّﻜُﻢْ ﻣَﺴْﺆﻭﻝ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ، ﺍﻹِﻣَﺎﻡُ ﺭَﺍﻉٍ ﻭَﻣَﺴْﺆﻭﻝٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ، ﻭَﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ ﺭَﺍﻉٍ ﻓِﻲ ﺃَﻫْﻠِﻪِ ﻭَﻫُﻮَ ﻣَﺴْﺆﻭﻝٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ، ﻭَﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺭَﺍﻋِﻴَﺔٌ ﻓِﻲ ﺑَﻴْﺖِ ﺯَﻭْﺟِﻬَﺎ ﻭَﻣَﺴْﺆﻭﻟَﺔٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻬَﺎ، ﻭَﺍﻟْﺨَﺎﺩِﻡُ ﺭَﺍﻉٍ ﻓِﻲ ﻣَﺎﻝِ ﺳَﻴِّﺪِﻩِ ﻭﻣَﺴْﺆﻭﻝٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ، - ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﺣَﺴِﺒْﺖُ ﺃَﻥْ ﻗَﺪْ ﻗَﺎﻝَ : ﻭَﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ ﺭَﺍﻉٍ ﻓِﻲ ﻣَﺎﻝِ ﺃَﺑِﻴﻪِ ﻭَﻣَﺴْﺆﻭﻝٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ - ﻭَﻛُﻠُّﻜُﻢْ ﺭَﺍﻉٍ ﻭَﻣَﺴْﺆﻭﻝٌ ﻋَﻦْ ﺭَﻋِﻴَّﺘِﻪِ ))
Lallai kowa me kiwo ne, kuma se an titsiye shi game da kiwon da aka ba shi a Lahira, KUMA SE YA ANSA.
.
Kukan kurciya dai jawabi ne!
.
****************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, ya bamu ikon farkawa daga dogon baccin da muke yi a yau na fifita gajeruwar rayuwa a kan rayuwar har abada.
Ameen

Post a Comment (0)